Wayyo Gida Na: Jigon PDP Ya Kai Kuka, Gwamnatin APC Za Ta Rusa Masa Muhalli

Wayyo Gida Na: Jigon PDP Ya Kai Kuka, Gwamnatin APC Za Ta Rusa Masa Muhalli

  • Uche Rochas ya komawa Ubangijinsa bayan ganin gwamnati ta buga tambari da nufin ruguza gidan da yake zama
  • ‘Dan siyasar ya nuna ya tanadi duk wasu takardu da ake bukata kafin ya gina gidan, amma duk da haka bai kubuta ba
  • Idan ya yi sa’a, hukuma za ta ruguza bangaren katangar gidan domin bude hanyar ruwa ba tare da yi masa barna ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Uche Rochas wanda jagora ne a jam’iyyar PDP a Kudancin Najeriya, ya fito ya na kokawa game da shirin ruguza gidansa.

Arch. Uche Rochas ya na cikin ‘yan siyasan da ke yawan amfani da dandalin Twitter, a nan ne ya bayyana abin da yake faruwa.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 8 da ake zargin sun tare a Abuja da wasu garuruwa sun bar jihohinsu

‘Dan siyasar ya ce bayan shekara da shekaru ya na rayuwa a gidansa, sai rana daya kwatsam ya ji gwamnati za ta ruguza shi.

Gida.
Wani gida (dabam) da aka rusa Hoto:www.dataphyte.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a ruguza gidajen mutane a Legas

Rochas ya nuna babu wani laifi da ya yi, yake neman alakanta matakin da sabanin siyasa saboda bai tare da APC mai-ci a Legas.

Shi kan shi Arch. Rochas wanda yake goyon bayan Atiku Abubakar ya ce ana shirin rusa gidajen makwabtansa a rukunin gidajen.

A cewarsa gwamnatin Legas ce da hadin-kan hukumar FHA ta tarayya su ka dauko aikin rusa wasu gine-gine da sunan saba ka’ida.

Laifin me Uche Rochas ya aikata?

Sai dai mutane sun maida masa martani cewa gwamnati ta bayyana dalilin daukar wannan mataki, ta rubuta baro-baro a gidan.

Hujjar da gwamnati ta bada shi ne ginin ya bi ta kan hanyan ruwa, saboda haka za a rusa shi domin hakan ne zai amfani al’umma.

Kara karanta wannan

Kogi: "Na tsallake rijiya da baya sau 30" Ɗan takarar Gwamna a arewa ya faɗi mutanen da aka kashe

"Bayan samun duk wani izini har da takardar mallakar CofO daga hukumar kula da gidaje, duk da haka sai ga sanarwar ruguzawa bayan shekaru bakwai ina zaune a nan.
An yi wa sauran gine-gine shaida a rukunin gidajen za a rusa su. Ina tunanin kun san dalilin."

- Uche Rochas

Rochas ya kare Gwamnatin Abacha

Ana da labari Uche Rochas ya wanke Marigayi Janar Sani Abacha daga zargin da ake yi masa na satar kudi a lokacin ya na karagar mulki.

‘Dan siyasar ya ce babu wata satar da Abacha ya yi, a cewarsa dukiyar da ake ikirarin Marigayi Abacha ya sata, kudin man da Najeriya ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel