Matawalle Ya Fito da Tsofaffin Takardu, Ya Tona Cin Amanar da Dauda Ya Yi wa Zamfara

Matawalle Ya Fito da Tsofaffin Takardu, Ya Tona Cin Amanar da Dauda Ya Yi wa Zamfara

  • Bello Muhammad Matawalle ya yi karin haske a kan rigimar da ake yi da shi da sabuwar gwamnatin jihar Zamfara
  • Tsohon Gwamnan ya ce hana Dauda Lawal Dare hanyar da zai soke miliyoyin kudi ne ya fara hada shi fada da shi
  • Matawalle ya yi ikirarin ya ba kamfanin Gwamna mai-ci kwangilar sama da N500bn domin shigo da takin zamani

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - A hira da aka yi da shi a tashar DCL Hausa, Bello Muhammad Matawalle ya yi bayani mai tsawo kan rikicinsa da Dr. Dauda Lawal Dare.

Wani masoyin Kashim Shettima mai suna I. U Wakili ya wallafa bangaren hirar a shafinsa na Twitter, ya ce ba saboda talakawa ake fadan ba.

Kara karanta wannan

Abin da ya faru bayan an sace daliban Jami'ar Zamfara – Matawalle ya magantu

Bello Matawalle
Bello Matawalle ya na fada da Gwamna Dauda Lawal Hoto: @Bellomatawalle1
Asali: Twitter

Matawalle: "Dauda ya kawo bashin N30bn"

Bello Muhammad Matawalle ya zargi Dauda Lawal Dare da yi wa Zamfara hanyar samun bashin N30bn saboda abin da zai shigo masa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar tsohon Gwamnan, Dauda Lawal ya hada shi da ma’aikatan wani banki da su ka ba kananan hukumomin jihar Zamfara aron biliyoyi.

Bayan an gama komai, sai Matawalle ya ce ya lura ana cire kudin ruwa da yawa, da ya nemi bankin su yi bayani, sai aka kira sunan Dauda.

Ganin an karkatar da Naira miliyan 300 zuwa ga aljihun magajinsa, Ministan tsaron ya bukaci a fasa karbar fashin, ya ce silar fadan kenan.

Kwangilar taki da Matawalle ya ba Dauda

Kamar yadda ya nuna a bidiyo, karamin Ministan tsaron ya ce a lokacin ya na gwamna, Dauda Lawal ya nemi kwangilar taki a Zamfara.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa Sun Tsoma Baki a Rigingimun Dauda/Matawalle da BUA/Dangote

Duk da mutane da-dama sun nemi kwangilar, Matawalle yake cewa ya ba kamfanin Dauda Dare kwangilar kawo taki ganin shi ‘dan Zamfara ne.

Abin da Matawallen ya fada a hirar shi ne Gwamna mai-ci ya yaudare shi, an yi ta kai ruwa-rana kafin ya cika alkawarinsa bayan wata bakwai.

Tsohon Gwamnan ya ce ya yi wa ‘dan kasuwan alfarma, ya ba shi satifiket domin kamfaninsa ya samu kudin kawo kaya, amma duk a banza.

Dauda ya yaudari Gwamnatin Matawalle?

Daga karshe Ministan yake cewa Dauda ya rika addabar shi da Kwamishinoninsa da waya a biya shi kudi, bayan da farko ya nuna bai bukatar sisi.

Domin samun wannan kwangila ta N504bn, Matawalle ya ce Dauda ya yaudare shi, har ya na nuna masa Godwin Emefiele ya ba shi kwangiloli.

NEF za ta yi wa Matawalle da Dauda sulhu

Mai girma Dauda Lawal da Bello Mohammed Matawalle su na rigama tun da aka yi canjin gwamnati a bana, ana da labari za a dinke barakar.

Kara karanta wannan

An Damfari ‘Dan Kasuwa An Sulale da Motar N6.2m Ana Tsakiyar Gwajin Lafiyar Inji

Shugaban kungiyar NEF, Farfesa Ango Abdullahi ya ce mutanen Zamfara na wahala, amma an biyewa rikicin siyasan da bai da amfani a gare su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel