Gwamnoni 8 da Ake Zargin Sun Tare a Abuja da Wasu Garuruwa Sun Bar Jihohinsu

Gwamnoni 8 da Ake Zargin Sun Tare a Abuja da Wasu Garuruwa Sun Bar Jihohinsu

  • Duk da gwamnoni su ne ke da alhakin kula da tsaro a jihohinsu, ana tuhumar wasu daga cikinsu da rashin zama a gida
  • Wasu gwamnoni su kan yi nesa da talakawansu saboda ayyuka da suke bijiro masu, a dalilin hakan su ka zuwa Abuja
  • Akwai wadanda uzurin tsaro ko rashin lafiya ya jawo sun fice daga jihohinsu Najeriya saboda neman magani a asibiti

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Akwai wasu gwamnonin jihohi da ake tuhuma da rashin zama a garuruwansu, sun koma wurare dabam da inda ake bukatarsu.

Rahoton nan ya tattaro jerin wadannan gwamnoni kamar yadda Punch ta kawo wasunsu:

Gwamnoni 8
Wasu Gwamnonin Jihohi Hoto: @Shettimasman, @RotimiAkeredolu da @UbaSaniUS
Asali: Twitter

1. Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq (APC)

Gwamnan Kwara bai cika zama a gida ba, jam’iyyar PDP mai hamayya ta na zargin ba a ganinsa, tun da ya zama shugaban kungiyar NGF.

Kara karanta wannan

Wayyo Gida Na: Jigon PDP Ya Kai Kuka, Gwamnatin APC Za Ta Rusa Masa Muhalli

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za ayi masa uzuri domin ayyuka da-dama ya kan jawo shugabannin gwamnoni su bar gida, an ga haka a lokacin Abdulaziz Yari a Zamfara.

2. Gwamna Mohammed Inuwa Yahaya (APC)

Shi ma Gwamnan jihar Gombe bai tsira ba, ‘yan adawarsa na jifansa da cewa bai zama a gida, ana zargin mafi yawan lokaci ya na nesa da Gombe.

Uzurin da za a iya ba Gwamna Inuwa Yahaya shi ne ya na jagorantar gwamnonin Arewa.

3. Gwamna Ahmad Aliyu (APC)

Jaridar ta ce mazauna su na kukan cewa irin abin da ya faru a zamanin Aminu Waziri Tambuwal ya na maimaita kan shi a mulkin APC a Sokoto.

Wasu mazauna jihar Sokoto sun ce ba a ganin Ahmad Aliyu, kullum ya na birnin Abuja.

4. Gwamna Dauda Lawal (PDP)

Tun bayan zamansa Gwamna, ana zargin Gwamna Dauda Lawal bai cika zama a Gusau ba, hakan ya jawo abin magana daga mutanen Zamfara.

Kara karanta wannan

Kogi: "Ni ake nema a kashe" Ɗan takarar Gwamna ya tona shirin Gwamnan APC a jihar arewa

A wata hira da aka yi da Kwamishinan Zamfara, ya bayyana cewa gwamnan ya na fadi-tashi ne saboda ya ceto jihar daga cikin wayyo Allah.

5. Gwamna Yahaya Bello (APC)

Mai girma Yahaya Bello ya na cikin gwamnonin da aka rahoto cewa ana yawan ganinsu a Abuja har sai da ta kai ya nemi takarar shugaban kasa.

Sai dai yanzu Gwamnan ya maida hankali a gida musamman saboda kokarin ganin Ahmed Usman Ododo ya lashe zaben da za ayi a Nuwamban nan.

6. Gwamna Uba Sani (APC)

A gwamnonin da suka karbi mulki a 2023, Uba Sani ya shiga sahun wadanda ake zargin sun kauracewa mutanensu, sun biyewa siyasa a Abuja.

Masu amfani da kafofin sadarwa na zamani suna yawan kokawa da halin da Kaduna ta ke ciki bayan Nasir El-Rufai ya sauka daga kan mulki.

7. Gwamna Mai Mala Buni (APC)

Mutanen jihar Yobe sun saba korafi a kan yadda Mai Mala Buni ya ke yawo a maimakon ya maida hankali a kan al’ummar da su ka zabe shi a 2019.

Kara karanta wannan

Zamfara: Matawalle ya bayyana dalilin da yasa Gwamna Lawal ke 'kulla masa makirci'

Legit ta fahimci cewa koken ya fi yawa kafin zaben 2023 domin kuwa an yi lokacin da aka bar wa Gwamna Buni rikon jam’iyyar APC nakasa a Abuja.

8. Gwamna Rotimi Akeredolu (APC)

Shi kuwa Mai girma Rotimi Akeredolu ya na fama da rashin lafiya ne, wannan ya jawo ya shafe watanni ya na jinya a kasar Jamus a shekarar nan.

Ko bayan dawowar Gwamnan, sai aka ji ya wuce Ibadan a maimakon ya zauna da mutanensa, shi ne shugaban gwamnonin Kudu maso yamma.

Shari'ar zaben Gwamnan Kano

Ku na da labari tsohon Ministan shari'an Najeriya, Akinlolu Olujinmi, SAN ne ya zama babban lauyan Nasiru Gawuna a shari'ar zaben Kano.

Lauyan ‘dan takaran ya zama SAN tun 1997, ya fara yin aikin Lauya kuma tun a shekarar 1979, ana sa ran shi zai jagoranci nasarar APC a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng