Kwamishina Ya Fallasa Yadda Matawalle Ya yi Watsa-Watsa da Jihar Zamfara a Bidiyo

Kwamishina Ya Fallasa Yadda Matawalle Ya yi Watsa-Watsa da Jihar Zamfara a Bidiyo

  • Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki ya koka a kan halin da su ka ji mulkin jihar Zamfara a Mayun 2023
  • Abdul Malik Gajam ya shaida cewa an wawuri dukiyar al’umma a gwamnatin Bello Matawalle ba tare da an yi aikin kwarai ba
  • Duk da rashin kokarinsa a bangaren tsaro a cewar Gajam, sabuwar gwamnatin tarayya ta ba Matawalle kujerar Ministan tsaro

Zamfara - Abdul Malik Gajam ya cigaba da yin bayanai a game da yadda gwamnatin Dauda Lawal Dare ta karbi mulki a jihar Zamfara.

A jeringiyar bidiyoyi da ya fitar a dandalin Twitter, Kwamishinan kasafin kudin na Zamfara ya yi maganar yadda Bello Matawalle ya yi mulki.

Kafin nan, Gajam ya ce jiharsu ta na baya sosai a yau a bangarorin cigaba baya ga tulin bashi da aka bar gwamnatin ta na biya duk wata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malam Dikko ta bankaɗo wasu illoli da ƴan bindiga suka yi a Jihar Katsina

Gwamnatin Matawalle
Gwamnan Zamfara yana sukar Gwamnatin Matawalle Hoto; Dauda Lawal
Asali: Facebook

Gajam: "Matawalle ya cinye kudin Zamfara"

Kwamishinan kasafin kudin ya ce Gwamnatin Matawalle ta ki fitar da kasonta na fanshon ma’aikata, a karshe ta cinye kudin da aka tara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Gajam, baya ga ruwan sha da hanyoyi, Gwamna Dauda Lawal Dare na neman kudi domin inganta bangaren kiwon lafiya a jihar.

“Jihar ba ta da kudi, an kashe kudinta, an watse kudinta, an ci mata bashin hankalin da ba ta ma iya yin wani abin.
Mutane sun koma suna yin cuta wajen daukar ma’aikata da albashi, mutum guda ya amshi albashin mutum 2-3.”

- Abdulmalik Gajam

Ya aka yi Matawalle ya zama Ministan tsaro?

A fai-fen, Gajam ya ce gwamnatin tarayya ta nada mutumin da ya rabawa ‘yan bindiga motoci kuma ya ajiye su a fadarsa a matsayin Minista.

Wasu zargin da aka jefi tsohon Gwamnan da su, sun hada da karkatar kudi a kwangilolin bogi da sayen motocin sama da Naira biliyan 15.

Kara karanta wannan

An waiwayi mutanen da ƴan bindiga suka addaba a Zamfara, Gwamna ya karɓo musu tallafi mai tsoka

Gajam bai tsaya a nan ba, ya ce sai da Matawalle ya zama shugaban kwamitin tsaro a majalisar wakilai ne aka fara fama da rikicin Boko Haram.

Kwamishinan yake cewa ba su da kudin magance matsalar tsaro alhali ana fama da bashin albashin watanni uku da gwamnatin baya ta ki biya.

Zargin badakalar Gwamnatin Matawalle

A baya an ji labarin yadda ake zargin Gwamnatin Matawalle ta biya duka kudin aikin kwangilar gina gidajen Gwamna tun ba a fara ayyukan ba.

Dauda Lawal ya na zargin an yi watsi da ka’idojin kwangila da gan-gan saboda a sace dukiyar jihar Zamfara na tsawon shekara da shekaru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel