Shari’ar Kano: Wanda Ya Buga da Yar’adua, Ya Kare El-Rufai a Kotu Ya Zama Lauyan Gawuna

Shari’ar Kano: Wanda Ya Buga da Yar’adua, Ya Kare El-Rufai a Kotu Ya Zama Lauyan Gawuna

  • Akinlolu Olujinmi (SAN) ya tsayawa Nasiru Yusuf Gawuna a kotun daukaka kara a shari’ar zaben Gwamnan Kano
  • Lauyan mai shekara 75 ya yi digiri a jami’ar jami’ar Obafemi Awolowo, su ne su ka kafa Olujinmi and Akeredolu a 1986
  • A lokacin da Olusegun Obasanjo ya zama shugaban kasa, ya nada Olujinmi domin ya zama Ministan shari’a kuma AGF

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Wanda yake tsayawa kare Nasiru Yusuf Gawuna a kotu a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano shi ne Cif Akinlolu Olujinmi (SAN).

A rahoton nan, Legit ta tattara ‘yan takaitattun bayanai game da Akinlolu Olujinmi (SAN), za a iya samu wasu bayanan a shafinsa na ICC.

Gawuna
Akinlolu Olujinmi (SAN) ya tsayawa Nasiru Gawuna Hoto: Adekunle Olanipekun
Asali: Youtube

1. Haihuwa da karatun Lauyan Gawuna

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi kamu, tsohon minista da ɗan takarar gwamna sun ƙara yi wa jam'iyyar PDP babban lahani

An haifi Akinlolu Olujinmi ne a shekarar 1948 a garin Ibadan da ke jihar Oyo. Olujinmi ya yi karatun shari’a a jami’ar Obafemi Awolowo a Ile-Ife.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Aikin lauyan Akinlolu Olujinmi

A shekarar 1979 aka kira Olujinmi zuwa makarantar koyon aikin lauyoyi. Bayan nan ai ya fara aiki a kamfanin NISER, daga baya ya koma UNIBADAN.

Zuwa 1986, Lauyan sun bude kamfaninsu mai suna Olujinmi and Akeredolu. Ofishinsu ya na titin Muhammadu Buhari a unguwar Garki a Abuja.

3. Yaushe Olujinmi ya zama SAN?

Olujinmi ya na cikin Lauyoyin da aka yi wa karin matsayi zuwa SAN a shekarar 1997. Samun lambar SAN na nufin ya gawurta a harkar shari’a.

4. Zama Ministan shari’a a 2003

Akinlolu Olujinmi, SAN ya rike Ministan shari’a na shekaru biyu tsakanin 2003 da 2005 a lokacin da Shugaba Olusegun Obasanjo ya ke mulki.

Kara karanta wannan

Makinde: Gwamnan PDP ya ciri tuta, ya yi ƙarin albashi mai tsoka ga ma'aikata da 'yan fansho

Lauyan ya maye gurbin Kanu Agabi SAN, bayan an cire shi kuma sai aka nada Bayo Ojo SAN.

5. Wanda Gawuna ya dauko ya yi aiki a Kotun ICC

Kwarewar Lauyan ta sa har ya taba gabatar da takarda a matsayin bako mai jawabi a zauren babban kotun Duniya watau ICC tun a 2005.

6. Shari’o’i kafin zama Lauyan Gawuna

Akinlolu Olujinmi ne ya kai kara a lokacin da Ummaru ‘Yaradua ya bar Najeriya ya na shugaban kasa ba tare da ya nada shugaban rikon kwarya ba.

Lauyan ya tsayawa Cecelia Ibru lokacin da Sanusi Lamido Sanusi ya maka ta a kotu bayan ya zama Gwamnan babban bankin Najeriya na CBN a 2009.

Da aka taso Nasir El-Rufai a gaba a Yulin 2009, lauyan ne wanda ya kare shi. An zargi tsohon Ministan da badakalar filaye da ya ke rike da Abuja.

7. Kare Jam'iyyar APC a Kotun zabe

Kara karanta wannan

Babu maganar komawa Majalisa bayan Ministar Tinubu ta fado ta kai a Kotun zabe

Kafin yanzu, lauyan ya yi shari’a a kotu a matsayin lauyan zabe na APC, shi ne kan gaba wajen kare Biodun Olujunmi da aka yi zaben Gwamnan Ekiti.

Wole Olanipekun ya tsayawa Abba Kabir Yusuf

Labari ya zo cewa Lauyan Abba Kabir Yusuf ya ce tun farko yin hukuncin zabe ta Zoom da aka yi domin raba gardama a Kano ya sabawa doka.

Wole Olanipekun ya na ikirarin ba ayi wa NNPP adalci a Kano ba, ya nemi a soke nasarar APC, inda Olujunmi ya zargi jam’iyya mai-ci da magudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel