Kotun daukaka kara ta tanadi hukunci domin raba gardama a tsakanin Gwamna Abba da Nasiru Gawuna
- Kotun ɗaukaka ƙara ta shirya raba gardama a ƙarar da gwamnan Kano ya ɗaukaka yana ƙalubalantar hukuncin kotun zaɓe
- Kotun zaɓen dai ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen
- A ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, kotun ɗaukaka ƙarar ta tanadi hukuncinta kan ƙarar inda ta ce za a sanar da ranar yanke hukunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
FCT, Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta tanadi hukunci kan ƙarar da gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya shigar, yana kalubalantar tsige shi da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano ta yi, cewar rahoton The Punch.
A ranar 20 ga watan Satumba ne kotun zaɓen ta soke zaɓen Gwamna Yusuf inda ta bayyana cewa ƙuri'unsa 165,663 ba su da inganci.
Kotun ta ce hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ba ta sanya hannu ko tambari a kan ƙuri'un ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakamakon haka, ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, Nasiru Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan.
Rashin gamsuwa da hukuncin, Gwamna Abba ya ɗaukaka ƙara a kotun ɗaukaka ƙara inda ya buƙaci kotun ta yi watsi da hukuncin kotun zaɓen.
Jaridar Daily Trust ta ce, kotun ɗaukaka ƙarar ta tanadi hukuncinta ne a ranar Litinin, 6 ga watan watan Nuwamban 2023.
Ya ya zaman kotun ya kasance?
A zaman kotun na ranar Litinin, Wole Olanipekun, SAN, lauyan Gwamna Yusuf, ya buƙaci a yi watsi da hukuncin kotun zaɓen.
Da yake nuna adawa da hukuncin da aka yanke na soke ƙuri'un, babban lauyan ya ce wannan shi ne karo na farko a tarihi da wata kotu za ta soke zaɓen da aka yi kan rashin sanya hannu a bayan ƙuri'u.
Ya ce kotun ta yi kuskure, inda ya ƙara da cewa, wannan shi ne karo na farko da wata jam’iyyar siyasa za ta shigar da ƙara ba tare da shigar da ɗan takararta a cikin ƙarar ba, kuma a bayyana ɗan takarar a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.
Sai dai, lauyan jam'iyyar APC Akin Olujimi SAN ya mayar da martani yana mai cewa kotun daukaka ƙara ta bayyana ƙarara cewa rashin sanya hannu kan ƙuri'u maguɗin zaɓe ne.
Ya ƙara da cewa dokokin INEC sun bayyana abin da malaman zaɓe za su yi a lokacin kaɗa ƙuri’a, inda ya ce dole ne a sanya hannu a bayan ƙuri'u da kwanan wata.
Daga baya kotun ɗaukaka karar ta tanadi hukuncinta, inda ta ce za a ranar da ranar yanke hukunci ga ɓangarorin.
Za a Fara Sauraron Daukaka Karar Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun ɗaukaka ƙara ta sanya ranar da za ta fara sauraron ɗaukaka ƙarar da Gwamna Abba ya yi kan shari'ar zaɓen gwamnan Kano.
Kotun ta sanya ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba matsayin ranar da za ta fara jin ba'asi a ƙarar da gwamnan ya ɗaukaka.
Asali: Legit.ng