Abin Da Ya Sa Aka ga Gwamnonin PDP 3 Wajen Wike, Hadimin Atiku
- Gwamnonin da su ka tashi su ka ziyarci Nyesom Wike su na cigaba da shan suka, ana yi masu kallon butulu a PDP
- Demola Rewaju ya ce neman alfarma ya kai wadannan Gwamnonin Jihohin PDP wajen Ministan saboda shari’arsu a kotu
- An yi dace, kowane daga cikin jagororin adawar da aka gani tare da Ministan na Abuja, ya na fuskantar shari’ar zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Demola Rewaju ya na cikin wadanda su ka yi tir da ziyarar da Gwamnonin PDP su ka kai wa Ministan birnin tarayya, Nyesom Wike.
Ganin ya karbi mukami a gwamnatin APC da Bola Ahmed Tinubu ya ke jagoranta, wasu ‘yan PDP su na jin haushin tsohon gwamnan jihar Ribas.
Demola Rewaju wanda ya na cikin Hadiman ‘dan takaran PDP 2023, Atiku Abubakar, bai ji dadin ganin Gwamnoninsa a ofishin Nyesom Wike ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta taso Gwamnonin PDP a gaba?
‘Dan siyasar ya ce ba komai ya jawo hakan ba illa akasarin gwamnonin nan duk su na fuskantar shari’o’in zabe wanda za su kai su gaban koli.
Mai taimakawa Atiku Abubakar a kan dabarun sada sadarwa ya ce Ahmadu Fintiri ya sha da kyar a hannun Aisha Binani a zaben Gwamna.
Shi kuwa Bala Mohammed ya nemi tikitin shugaban kasa tare da Wazirin Adamawa a 2022, a karshe kotu ta cece shi ya sake takara a Bauchi.
Na uku a tawagar shi ne Gwamna Caleb Mutfwang na Filato, inda jam’iyyar PDP ta ke ta rasa kujerun da ta lashe a sakamakon hukuncin kotu.
Maganar Demola Rewaju
"Saura kiris (Aisha Dahiru) Binani ta sha gaban (Gwamna Ahmadu) Fintiri, Gwamna Mutfwang ya na Filato, inda abubuwa ba su yi masa kyau ba.
Bala Mohammed ya je takarar shugaban kasa kafin ya dawo ya karbe tikitin daga hannun ‘wanda ya lashe zabe’ – irin na Ahmad Lawan a kotu."
-Demola Rewaju
Rewaju yake cewa ‘yan jam’iyyar ta sa sun ziyarci Wike ne saboda yadda abubuwa su ka tabarbare, a cewarsa ba su san lokacin siyasa ya wuce ba.
Nyesom Wike v 'Yan Majalisan Ribas
Rahoto ya zo cewa Nyesom Wike ya zauna da Sanatoci da ‘yan majalisar wakilan tarayya daga Ribas a yunkurin yi masa sulhu da Gwamnansa.
Ministan harkokin birnin Abujan ya jaddada cewa ba arzikin Ribas yake hange ba, ya ce babban matsalansa ita ce siyasar da ake neman lalatawa.
Asali: Legit.ng