Nyesom Wike Ya Zauna da ‘Yan Majalisa, Ya Jaddada Sharudan Sasantawa da Gwamnan Ribas

Nyesom Wike Ya Zauna da ‘Yan Majalisa, Ya Jaddada Sharudan Sasantawa da Gwamnan Ribas

  • Nyesom Wike ya zauna da Sanatoci da ‘yan majalisar wakilan tarayya daga Ribas a yunkurin yi masa sulhu da Gwamnansa
  • Ministan harkokin birnin tarayya Abujan ya jaddada ba arzikin Ribas yake hange ba, ya ce babban matsalansa siyasar gida
  • Wike ya fadawa ‘yan majalisar cewa babu azabar da bai gani ba a lokacin da yake adawa da gwamnatin Muhammadu Buhari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Ministan harkokin birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya maida amsa ga masu zargin cewa ya na kwadayin dukiyar jihar Ribas.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta ce Nyesom Wike ya karyata zargin da ake yi masa na neman 25% daga cikin dukiyar gwamnatin Ribas.

Ministan Abujan ya ce masu wannan magana sun jahilci lamarin, ya yi wannan karin haske ne da ya zauna da ‘yan majalisa daga jiharsa.

Kara karanta wannan

Wike ya karyata rade-radi, ya shaidawa Gwamnoni silar rigimarsa da Gwamnan Ribas

Nyesom Wike
Nyesom Wike da 'Yan Majalisan Ribas Hoto: nannews.ng
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin Ribas: Nyesom Wike v 'Yan Majalisa

Wike ya gana da Sanatoci uku da ‘yan majalisar wakilan tarayya 11 da ke wakiltar mazabun Ribas a majalisun tarayya a garin Abuja.

Makasudin zaman shi ne dinke barakar da ke tsakanin Wike da gwamna Siminalayi Fubara.

Tawagar Sanatoci da ‘yan majalisa da ta hadu da Wike a ranar Alhamis ta dauki alwashin za a hada-kai ayi aiki tare domin cigaban Ribasawa.

Premium Times ta ce Kingsley Chinda ya yi jawabi a madadin tawagar, ya kara da godewa gudumuwar tsohon gwamnan lokacin zaben 2023.

Me Wike ya fadawa 'Yan Majalisa?

"Idan ka yi kura-kurai, za mu kira ka mu fada maka ka na kuskure. Ka dauka da kwakkyawan manufa cewa mun ankarar da kai ka saki layi.
Amma idan mu ka kira, ka da ka dauka mu na neman 25% ko wani kason baitul-mali ne.

Kara karanta wannan

"Ba matsala ne ba idan an samu rashin jituwa tsakanin ɗa da mahaifi", Gwamna Fubara

Dukkanmu daya ne. Mun gina tafiyar siyasar nan na tsawon lokaci, tun 2015, kuma mun yi nasara.
A matsayin jam’iyyar adawa tun 2015, na ga azaba. Gwamnatin tarayya ta yake ni ta gaba da baya da tsakiya, amma da taimakonku, mu ka tsira.
Idan aka yi aiki tare, za a ga zai yi wahala wani daga waje ya karya ku a gidanku.

- Nyesom Wike

Gwamnonin PDP sun gana da Wike

Kafin nan ana da labari gwamnonin PDP sun gana da ‘dan siyasar duk a yunkurin ganin an hana majalisar dokoki tsige sabon gwamnan Ribas.

Ministan ya ce ba za ta yiwu Simi Fubara a matsayinsa na sabon gwamnan jihar Ribas ya jawo abokan fadansu bayan sun yi galaba a zabe ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng