Wuta Ta Kunno Kai a APC, Ana Rikici Tsakanin Minista da Shugaban Majalisar Tarayya
- Rt. Hon. Benjamin Okezie Kalu ya karyata masu neman jifansa da laifin rigima da Nkeiruka Onyejeocha wanda Minista ce a gwamnati
- Wani hadimin Mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayyan ya ce mai gidansa bai samu sabani da Ministar kwadagon ba
- Jawabin da aka fitar ya karyata zargin da ake yi wa ‘dan siyasar na yin fada da takwararsa wanda su ka fito daga jihar Abia a APC
Abuja - Ben Kalu ya ce shi dai babu wata rigima tsakaninsa da karamar Ministar kwadago da samar da ayyuka, Nkeiruka Onyejeocha.
Honarabul Benjamin Kalu ya nuna akwai alaka mai karfi tsakaninsa da Nkeiruka Onyejeocha, The Cable ta fitar da rahoton a ranar Talata.
Mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayyan ya karyata zargin da ake yi masa na yi wa jam’iyyarsa ta APC mai ci zagon-kasa a gida.
Kalu v Onyejeocha: An sanar da APC, Ganduje
Shugaban wata kungiyar ‘yan siyasa, Usman Shuaibu ya fito ya na cewa Ben Kalu ya na yakar Onyejeocha, ya nemi APC ta dauki mataki a kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganin ta kai ana kira ga Dr. Abdullahi Ganduje da majalisarsa su ladabtar da shi, jaridar ta ce ‘dan majalisa ya wanke shi daga zargin nan.
Ben Kalu ya maida martani a jam'iyyar APC
Babban Sakataren yada labaran Mataimakin shugaban majalisar, Levinus Nwabughiogu, ya fitar da jawabi a matsayin raddi ga kungiyar.
Nwabughiogu yake cewa Kalu ya dauki Ministar tarayyar a matsayin wata ‘yaruwarsa kuma abokiyar aiki mai daraja a tafiyarsu ta APC.
Kamar yadda aka rahoto daga Vanguard, jawabin ya kuma ce Kalu ‘dan siyasa ne wanda ya damu da halin da matasa su ke ciki a al’umma.
Da gaske akwai rikici a Abia APC?
"Duk da ta yi aiki a tsohuwar majalisa, Rt. Hon. Benjamin Okezie Kalu bai da alakar siyasa kai-tsaye da Onyejeocha da har za su samu sabani.
Dukkanin jami’an sun fito daga mazabu dabam-dabam, saboda haka babu dalilin rikici.
Baya ga haka, Onyejeocha ta na aiki ne a bangaren zartarwa, shi kuma Kalu ya shagala da harkokin gabansa na dokoki a majalisar tarayya."
- Levinus Nwabughiogu
Takarar Timipre Sylva a Bayelsa
Ana da labari cewa Rose Oriaran-Anthony ta ce hukuncin da aka zartar a kotu kwanaki ya jawo INEC ta yi waje da takarar APC a Bayelsa.
An bar jam’iyyar APC babu ‘an takara a zaben Gwamnan Bayelsa saboda biyayya ga hukuncin da ya hana Timipre Sylva sake hawa kan mulki.
Asali: Legit.ng