Gaskiyar Abin da Ya Faru da Mu – Gwamna Ya Yi Maganar Harin da Aka Kai Masa

Gaskiyar Abin da Ya Faru da Mu – Gwamna Ya Yi Maganar Harin da Aka Kai Masa

  • Yahaya Bello ya samu lokaci ya gabatar da jawabi a game da abin da ya faru tsakanin tawagarsa da wasu jami’an tsaro
  • Gwamnan jihar Kogi ya ce akasin abin da aka rahoto, ba hari aka kai masa a lokacin da yake hanyar zuwa garin Abuja ba
  • Bello yake cewa sojojin da ke tsare hanya ne su ka samu sabani da rundunar ‘yan sandan da ke kula da tawagar motocinsa

Abuja - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya karyata rahotannin cewa an yi yunkurin hallaka shi a wani hari a yammacin Lahadi.

Kwamishinan yada labaran jihar Kogi, Kingsley Fanwo ya fitar da jawabi cewa an kai wa tawagar Gwamnan hari, har ta kai ya sha da kyar.

Amma da yake jawabi a wani bidiyo, Mai girma Gwamnan ya fayyace yadda abin yake.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Tsageru sun yi yunkurin kashe gwamnan APC a Arewa, bayanai sun fito

Gwamnan Kogi
Gwamnan Kogi, Alhaji Dr. Yahaya Bello, CON Hoto: @OfficialGYBKogi
Asali: Twitter

"Abin da ya faru" - Yahaya Bello

Alhaji Yahaya Bello ya shaidawa manema labarai cewa ‘yar matsala aka samu tsakanin ‘yan sandan da ke cikin tawagarda da kuma sojoji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan sabani da aka samu da rundunar sojojin da ke tsare babban titin ne aka zuzuta, Gwamnan ya ce kowanensu ya na bakin aikinsa ne.

An ji Gwamna Yahaya Bello ya jinjinawa jami’an tsaron a game da hadin-gwiwar da su ka yi wajen inganta tsaron rayuwa da dukiyar al’umma.

"An samu tsaro a Kogi" - Gwamna

Daily Trust ta rahoto Gwamnan ya na cewa kokarin jami’an ya inganta tsaro a Kogi.

Amma duk da yadda ya yaba masu, Bello ya yi kira ga shugabannin hukumomin tsaron su yi bincike a kan wuce-gona da irin wasu jami’ansu.

Alhaji Bello ya na so a dauki hukunci da matakin da ya dace kan jami’an da su ka zakalkale a lokacin ‘yar takaddamar da aka samu da tawagarsa.

Kara karanta wannan

Tattalin Arziki: Abin Da Cire Takunkumin CBN Yake Nufi Ga Manoma Da Abinci, Masani

Shirin zaben Gwamna a Kogi

A jawabin da ya gabatar a jiya, Mai girma Gwamnan na Kogi ya yi kira ga mutanen jiharsa su yi watsi da masu neman kawo masu tashin-tashina.

Game da zaben Gwamna da za ayi a Nuwamba, Bello ya yi alkawarin yin gaskiya da adalci, inda zai so 'dan takaran da ya tsaida ya yi galaba a APC.

Kokarin Gwamnan Kano

Rahoto ya zo cewa Gwamnan jihar Kano, Mai girma Abba Kabir Yusuf ya lale fiye da N1bn wajen biyawa Kanawa 57, 000 kudin NECO da NBTE.

Gwamnatin Abba Gida Gida ta yi rabon kayan karatu kuma za a samar da karin makarantu da ma’aikata a Kano domin inganta harkar ilmi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel