Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Bankin Masana'antu BOI Na Kasa

Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Bankin Masana'antu BOI Na Kasa

  • Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Dokta Olasupo Olusi a matsayin sabon shugaban bankin masana'antu na ƙasa BOI
  • Kakakin shugaban kasa ya ce hakan ya biyo bayan murabus din da tsohon Manajan Daraktan BOI ya yi bisa ra'ayin kansa
  • Ya buƙaci wanda aka naɗa ya tabbatar da yan Najeriya sun samu tallafi da damarmakin da suke buƙata a kasuwanci

FCT Abuja - Shugaba Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nada Dokta Olasupo Olusi a matsayin sabon Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Bankin Masana’antu (BOI).

Wannan sabon naɗi na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Alhamis kuma aka wallafa a manhajar X.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Bankin Masana'antu BOI Na Kasa Hoto: Bola Tinubu
Asali: Twitter

Ya ƙara da bayanin cewa wannan naɗin zai shafe tsawon shekaru huɗu a zangon farko. Sanarwan ta ce:

Kara karanta wannan

Ta Leƙo Ta Laɓe, Shugaba Tinubu Ya Yi Amai Ya Lashe Kan Naɗin Matashi a Matsayin Shugaban FERMA

"Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Dr. Olasupo Olusi a matsayin Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Bankin Masana’antu (BOI) na tsawon shekaru hudu (4) a matakin farko."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban BOI ya yi murabus

Sanarwan ta ƙara da bayanin cewa Tinubu ya yi wannam naɗin ne bayan tsohon shugaban bankin BOI, Mista Olukayode Pitan, ya yi murabus bisa ra'ayin kansa.

"Shugaban kasa ya aminta da nadin Dr. Olusi ne biyo bayan murabus din da tsohon Manajan Darakta na BOI kuma Babban Jami’in gudanarwa, Mista Olukayode Pitan ya yi."

Tinubu ya bukaci sabon shugaban BOI da ya tabbatar da cewa ‘yan Najeriya da ke gudanar da harkokin kasuwanci manasa'antu a sassa daban-daban sun samu dama da tallafi.

Har zuwa nadin nasa, Olusi ya yi aiki a matsayin kwararre a fannin tattalin arziki da harkokin kudi na bankin duniya a cikin shekaru 20 da suka gabata.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Sabon Shugaban EFCC da Wasu 2 da Tinubu Ya Naɗa, Bayanai Sun Fito

Tsakanin 2011 zuwa 2015, ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara kan tattalin arziki ga Ministar Tattalin Arziki kuma Ministar Kudi, Ngozi Okonjo-Iweala.

Majalisar Tarayya Ta Bukaci a Kara Wa Malaman Firamare, Sakandire da Jami'o'i Albashi

A wani rahoton kuma Majalisar wakilan tarayya ta bayyana matakan da ya kamata a ɗauka domin gyara ɓangaren ilimi a Najeriya.

Honorabul Abubakar Fulata, shugaban kwamitin ilimin jami'o'i ya yi kira da a ƙara wa malaman Firamare, sakandire da jami'o'i albashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel