Majalisar Tarayya Ta Bukaci a Kara Wa Malaman Firamare, Sakandire da Jami'o'i Albashi

Majalisar Tarayya Ta Bukaci a Kara Wa Malaman Firamare, Sakandire da Jami'o'i Albashi

  • Majalisar wakilan tarayya ta bayyana matakan da ya kamata a ɗauka domin gyara ɓangaren ilimi a Najeriya
  • Honorabul Abubakar Fulata, shugaban kwamitin ilimin jami'o'i ya yi kira da a ƙara wa malaman Firamare, sakandire da jami'o'i albashi
  • Ya ce duk ƙasar da ta ci gaba, tana koyar da ilimi ne a harsukan cikin gida amma a Najeriya ba haka abin yake ba

FCT Abuja - Kwamitin Majalisar Wakilai Tarayya kan Ilimin Jami'o'i ya yi kira da a kara albashi ga malaman makarantun firamare da sakandare da na jami'o'i.

Kwamitin ya ce kamata ya yi a riƙa biyan malaman Firamare N250,000, Malaman Sakandire N500,000 yayin da Malaman jami'a su riƙa samun miliyan ɗaya a matsayin albashi duk wata.

Majalisar Wakilai ta lalubo hanyar gyara ilimi a Najeriya.
Majalisar Tarayya Ta Bukaci a Kara Wa Malaman Firamare, Sakandire da Jami'o'i Albashi Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Shugaban kwamitin, Abubakar Fulata ne ya faɗi haka yayin jawabi a wajen taron yini daya na masu ruwa da tsaki kan bunkasa taswirar ilimin Najeriya (2023-2027), a Abuja ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Waiwayi Leburori, Ya Ce Zai Ɗauki Nauyin Karatunsu Har Su Gama Jami'a Bisa Sharaɗi 1

Mista Fulata ya ce yana da kyau malaman Najeriya su ji kwarin gwiwa ta hanyar biyan su kudaden da suka dace domin koyar da yara, Daily Nigerian ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakan da za a bi wajen gyara ilimi

Ɗan majalisar ya kuma jaddada buƙatar fassara dukkan litattafan darussan makarantu zuwa harsunan cikin gida domin ɗalibai su kamo takwarorinsu na duniya.

A cewarsa, gwamnatocin da suka shude sun yi iya bakin kokarinsu a fannin ilimin kasar nan amma duk da haka bai haifar da sakamakon da ake so ba.

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, Fulata ya ce:

“Abin damuwa ne cewa tun daga shekarun da suka gabata, yunƙurin da gwamnatocin baya suka yi don farfado da ilimi, ci gaban da suka kawo kaɗan ne, bai taka kara ya karya ba."

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabuwar Rundunar Tsaro Ta Jihar Katsina

"A duk faɗin duniya, ana amfani da harsunan cikin gida ne wajen koyarwa, idan ka je Burtaniya, ana koyar da ilimi da Turanci, haka a Faransa ana koyarwa tun daga matakin farko zuwa sama da Faransanci."
"A Najeriya ne ake koyar da karatu da Turanci, muna koyar da yaran mu da wani yare wanda ya kamata a ce da yarensu ake karantar da su, wannan ce matsalar mu."
“Dole ne Najeriya ta ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi. Ya zama wajibi mu sadaukar da akalla kashi 25 zuwa kashi 30 na kasafin kudin kasarmu ga ilimi."

Shugaba Tinubu Ya Soke Naɗin Matashin Shugaban Hukumar FERMA

A wani rahoton kuma Shugaba Tinubu ya soke naɗin da ya yi wa matashin injiniya a matsayin shugaban hukumar FERMA.

Dama naɗin da shugaban ƙasa ya yi wa matashin ɗan shekara 24 a duniya wanda bai jima da kammala digiri ba ya haddasa cece kuce mai zafi a faɗin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel