Bayan Afuwar Da Buhari Ya Yi Masa, Kotu Ta Ce a Biya Tsohon Gwamnan Taraba, Jolly Nyame, Kuɗinsa Na Fansho

Bayan Afuwar Da Buhari Ya Yi Masa, Kotu Ta Ce a Biya Tsohon Gwamnan Taraba, Jolly Nyame, Kuɗinsa Na Fansho

  • Kotun Masana’antu ta Kasa da ke Abuja ta umarci Gwamnatin Jihar Taraba ta biya Jolly Nyame da sauran wasu mutane uku kudin fanshonsu a ranar Talata
  • Dama Nyame da wasu mutane uku sun nemi kotu ta amso musu hakkinsu da ke hannun gwamnati, ko dai a cire a asusun gwamnati ko a siyar da kadarar gwamnatin
  • Kamar yadda alkalin ya ce, gwamnatin Jihar Taraba ta sanya hannu a kan takardar yarjejeniya ta biyansu kudin fanshon hakan ya sa ba ta da wani dalili da zai sa ta ki yin hakan

FCT, Abuja - A ranar Talata, Kotun Masana’antu ta Tarayya da ke Abuja ta umarci gwamnatin Jihar Taraba da ta biya Jolly Nyame kudin fanshonsa, Premium Times ta ruwaito.

Dama Nyame da wasu mutane uku - Uba Ahmadu, Abubakar Armayau da Bilkisu Danboyi - sun nemi gwamnati ta biya su bashin da su ke binta ta hanyar diba daga asusunta ko kuma siyar da kadara.

Kara karanta wannan

Daga korafi a Facebook: Mutumin da gwamnan APC ya daure saboda sukar gwamnatinsa ya kubuta

Bayan Afuwar Ba Buhari Ya Yi Masa, Kotu Ta Ce a Biya Jolly Nyame Kuɗinsa Na Fansho
Kotu Ta Ce a Biya Jolly Nyame Da Wasu Mutane Kuɗinsa Na Fansho. Hoto: Premium Times.
Asali: Depositphotos

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hukuncin Kotun Ma'aikata

A ranar Talata, Kotun Masana’antu ta Kasa ta umarci gwamnatin Jihar Taraba ta biya Nyame da sauran wadanda su ka yi kara akan bashin da su da su ke bin gwmanati.

Alkalin, Osatohanmwen Obaseki-Osaghae, kamar yadda Premium Times ta nuna ya yanke hukunci inda ya ce Gwamnatin Jihar Taraba ba ta musanta batun bashin wadanda su ka yi kara ba, kuma ta sanya hannu akan takardar kudin fanshonsu.

Kotun ta yi hukunci akan cewa takardar hanya ce ta dakatar da hukuncin kotun da ake sa rai. Dama tun farko alkalin ya yi fatali da kin amincewa da hukuncin da Babban Bankin Najeriya ya yi.

CBN ya kulubalanci kotu akan hukuncin

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kalubalanci hukuncin kotu dangane da shari’ar, inda CBN ya ce a matsayin shi na hukumar gwamnatin tarayya, Babbar Kotu za ta iya bayar da umarnin cirar kudi daga asusun gwamnati ko kuma siyar da kadarar gwamnati don a biya wani ba, kamar yadda Sashi na 251, 1(d) na kundin tsarin mulkin 1999 da Sashi na 84 na dokar Shariff & Civil Process, wacce ta yi alkalanci da doka ta 2 da 3 ta Tilascin Shari’a.

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Muka Yi Dirar Mikiya a Gidan Okorocha, EFCC Ta Magantu

Amma alkalin ya ce kin yardar da hukuncin da CBN ta yi ba ta da damar yin hakan.

Alkalin ya ce CBN ba ma’aikacin gwamnati ba ne balle ya yi amfani da Sashi na 84 na dokar Sheriff & Civil Process.

Kotun ta tsaya akan cewa ta na da damar tilasta amfani da da dokar siyar da kadara ko kuma cirar kudi daga asusun gwamnati akan shari’ar kudi.

Nyame ya samu wannan nasarar ne bayan sakin shi daga gidan yari akan wawurar kudin jama’a da ya yi lokacin ya na gwamna

Alkalin ya ce masu bin bashin a takardar kotun da su ka cika sun bayyana cewa kudinsu ya na hannun CBN.

A hukuncin Talata, Nyame ya samu nasara, duk da ya saci kudin jama’a a lokacin da ya ke gwamnan Jihar Taraba.

Nyame wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Taraba daga 1999 zuwa 2007, kuma an daure shi ne tsawon shekaru 14 akan sata a watan Mayun 2018 bisa hukuncin da Babbar Kotun Abuja ta zartar.

Kara karanta wannan

AK9Train: Miyagu sun tuntubi kakakin Sheikh Gumi, sun ba FG wa'adin kwana 7 ko su aiwatar da nufinsu

Sai dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai dade da yafe masa ba tare da wasu masu laifi, wanda hakan ya fusata ‘yan Najeriya da dama.

2023: Kwana Kaɗan Bayan Buhari Ya Musu Afuwa, An Yi Kira Ga Dariye Da Nyame Su Fito Takarar Shugaban Ƙasa

A wani rahoton, an bukaci tsaffin gwamoni - Jolly Nyame da Joshua Dariye - wadanda a baya-bayan nan Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa afuwa su shiga takarar shugaban kasa.

Dan takarar shugaban kasa daga yankin tsakiya a Najeriya, wato Middle Belt, Moses Ayom, ne ya yi wannan kirar a ranar Alhamis 21 ga watan Afrilu.

The Nation ta rahoto cewa Ayom, wanda shima dan takarar shugaban kasa ne a karkashin jam'iyyar APC ya yaba wa Shugaba Buhari bisa afuwar da ya yi wa tsaffin gwamnonin na Taraba da Plateau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel