Bukar Abba Ibrahim ya ci girma, ya janyewa Ibrahim Geidam

Bukar Abba Ibrahim ya ci girma, ya janyewa Ibrahim Geidam

Tsohon gwamnan jihar Yobe kuma sanata mai wakiltan Yobe ta yamma, Sanata Bukar Abba Ibrahim ya hakura ya janyewa gwamnan jihar na yanzu, gwamna Ibrahim Geidam a takaran kujeran majalisar dattawan Najeriya da za’a yi a shekarar 2019.

Wannan abu ya biyo bayan ganawa ta musamman da masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC na jihar Yobe sukayi a jiya Talata, 18 ga watan Satumba, 2018 a jihar.

Zaku tuna cewa sanata Bukar Abba Ibrahim ya sayi takardan takaran kujeran sanata na jam’iyyar APC inda yace ba zai janyewa Geidam da ya nuna ra’ayin son takara ba.

Bukar Abba Ibrahim ya ci girma, ya janyewa Ibrahim Geidam
Bukar Abba Ibrahim ya ci girma, ya janyewa Ibrahim Geidam
Asali: Depositphotos

Bayan ga haka, tsohon gwamnan ya mara goyon bayansa ga wanda mamabobi da shugabancin jam’iyyar suka zaba a matsayin dan takaran gwamnan jihar wanda a aymzu shine sakataren jam’iyyar APC ta kasa, Malam Mala Mai Buni.

KU KARANTA: Kwastam sunyi babban kamu a Gombe inda suka wace tramadol da Diazepam na N7m

Bayan ganawar, Sanatan yace: “ Wannan zamanin siyasa ne kuma munyi ganawa daban-daba. Wasu manema labarai sun dauki wasu kuma basu dauki wasu ba. Ak karshe dai mun yanke.

“Makonnin da suka gabata an yi wata ganawa na zaben yan takara a Damaturu amma ba’a gayyace mu ba kuma munyi korafi, amma mun yi sulhu. Mu tsintsiya ne madaurinki daya .”

Shi kuma gwamnan jihar ya nuna farin cikinsa kan wanna abu da ya faru, ya siffanta BUkar Abba Ibrahim a matsayin Uban siyasa a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel