Yobe @27: Tarihin Gwamnonin Jihar Yobe daga 1991 zuwa yau
Mun kawo maku jerin Gwamnonin da su kayi mulki a Jihar Yobe daga lokacin da aka kafa Jihar a cikin Agustan 1991 zuwa yanzu. Wikepedia tana da jerin wadanda su ka mulki Jihar a lokacin mulkin Soji da farar hula.
1. Sani Daura-Ahmed
AIG Sani Daura-Ahmed ne ya fara yin Gwamna a Jihar Yobe bayan Jihar ta balle daga Jihar Borno. Daura-Ahmad yayi mulki ne daga 1991 zuwa 1992 lokacin mulkin Janar Ibrahim Babanguda.
2. Bukar Abba Ibrahim
Sanata Bukar Abba Ibrahim ne ya karbi mulki daga hannun Sani Ahmad Daura a farkon 1992. Bukar Abba yayi mulki ne har zuwa karshen 1993 lokacin da aka hambarar da Gwamnatin kasar.
KU KARANTA: Gwamnati ta hana Kwankwaso wajen shirin kaddamar da takara
3. Dabo Aliyuhakkin
AIG Dabo Aliyu CON mni ne yayi mulkin Jihar Yobe na fiye da shekaru 3 daga 1993 har zuwa 1996. Aliyu ‘Dan Sanda ne wanda yayi mulki ne a lokacin mulkin Janar Sani Abacha.
4. John Ibiwari Ben Kalio
Guruf Kyaftin John Ibiwari Ben Kalio ya rike Gwamna a Yobe daga tsakiyar 1996 har 1998. An zargi Gwamnatin Ben Kalio da keta hakkin ‘Yan jarida a lokacin yana Gwamnan Jihar.
5. Musa Mihammed
Kanal Musa Mohammed ya mulki Jihar Yobe na ‘dan lokaci kadan bayan Kyaftin John Ben Kalio ya bar mulki. Mohammed ya sauka a 1999 lokacin da aka dawo mulkin farar hula a Najeriya.
6. Bukar Abba Ibrahim
Alhaji Bukar Abba Ibrahim ne ya sake karbar mulki a 1999 bayan an yi zabe. Bukar yayi Gwamna na shekaru 8 a karkashin Jam’iyyar ANPP wanda daga baya ya zama Sanata.
7. Mamman Bello Ali
Sanata Mamman B. Ali wanda ya karbi mulki a hannun Bukar Abba yayi Gwamna na shekaru 2 kafin ya rasu. Mamman Ali ya rasu ne a 2009 a wani asibiti a Kasar Amurka.
8. Ibrahim Geidam
Bayan cikawar Sanata Mamman B. Ali ne Mataimakin sa Ibrahim Geidam ya karbi karagar mulki. Geidam ya dare kujera ne tun 2009 inda ya karasa wa’adin har ya zarce sau 2.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng