Zaben 2023: Sharri Aka Yi Mani, Ban Goyi Bayan Atiku a Boye ba Inji Jigon APC

Zaben 2023: Sharri Aka Yi Mani, Ban Goyi Bayan Atiku a Boye ba Inji Jigon APC

  • Chukwudi Dimkpa ya wanke kan shi daga zargin da ake jifansa da shi na cin amana da kuma yin zagon-kasa
  • ‘Dan siyasar ya ce babu inda aka yi wani kus-kus da shi saboda ganin yadda za a taimaki takarar Atiku Abubakar
  • Jawabin Stephen Deegbara ya nuna Injiniyan ya bada gudumuwa domin APC ta yi galaba a kan PDP a jihar Ribas

Rivers - Chukwudi Dimkpa ya musanya zargin da ake yi masa na cewa ya na cikin ‘ya ‘yan APC da su ka taimaki jam’iyyar PDP a zaben 2023.

A safiyar Litinin, jaridar Sun ta rahoto Injiniya Chukwudi Dimkpa ya na cewa babu hannunsa a wajen yi wa Bola Ahmed Tinubu zagon-kasa.

Hakan ya zo ne bayan Cif Tony Okocha ya zargi wasu ‘yan jam’iyyar APC na reshen jihar Ribas da goyon bayan takarar Alhaji Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Dambarwar Satifiket: Farfesan Amurka Ya Fadi Takardun Da Ya Kamata Tinubu Ya Mika Ga INEC

APC..
'Dan APC wajen kamfe hoto: sunnewsonline.com
Asali: Twitter

An zargi Tony Okocha da kawo sabani a APC

Sa’ilin da ya hadu da Dr Abdullahi Umar Ganduje a sakatariyar APC, Tony Okocha ya kai karar wasu da ya ce sun ci amanar jam’iyya mai mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma a wani jawabi da ya fitar a jiya, Chukwudi Dimkpa, ya ce bai cikin wadanda su ka yi taro da PDP, ya gargadi Okocha a kan raba kan APC.

Chukwudi Dimkpa ya yi wa Tinubu aiki

Mai magana da yawun bakin ‘dan siyasar, Stephen Deegbara ya ce mai gidansa bai ci amana ba, ya bada gudumuwarsa a wajen nasarar APC.

Bai cikin duk wani taro da aka dauki wani mataki kamar yadda Okocha yake nunawa.
Mu na nuna cewa a matsayin cikakken ‘dan jam’iyyar APC, Injiniya Chukwudi Dimkpa ya bada lokacinsa karfinsa da dukiyarsa tare da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin APC tayi nasara a zaben karshen nan da aka gudanar.”

Kara karanta wannan

Shugabannin Jam'iyya 21 da Jiga-Jigai Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Arewa, Sun Faɗi Abinda Ya Ja Hankalinsu

- Stephen Deegbara

Su wa ake zargi sun bi Atiku a APC?

Chukwudi Dimkpa ya na cikin wadanda aka jefa da yakar APC ta karkashin kasa a Ribas, duk da Leadership ta ce da shi aka rika zuwa kamfe.

Sauran magoya bayan Rt. Hon. Rotimi Amaechi a siyasa da ake zargin sun yi wa PDP aiki a zaben shugaban kasa sun hada da Mista Tony Cole.

Dakuku Peterside wanda ya rike NIMASA ya na cikin wadanda ake tuhuma da laifi.

Yakin Wike vs Amaechi a Ribas

Kwanaki aka samu rahoto mutanen Nyesom Wike a jihar Ribas, sun yi zama da Abdullahi Umar Ganduje a sakatariyar APC da ta ke Abuja.

An yi wa Shugaban APC bayanin yadda Rotimi Amaechi ya taimaki Atiku Abubakar a zabe. Tsohon ministan kasar bai ce komai kan batun ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel