Rudani a APC, ‘Yan Jam’iyya Sun Tona Wadanda Su Ka Goyi Bayan Atiku a 2023

Rudani a APC, ‘Yan Jam’iyya Sun Tona Wadanda Su Ka Goyi Bayan Atiku a 2023

  • Magoya baya da wasu jagororin APC a Ribas sun zargi Rotimi Amaechi da shirya zagon-kasa
  • Tony Okocha da mutanensa sun ziyarci Shugabannin APC a karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje
  • ‘Dan siyasar ya fadawa NWC cewa Amaechi ya umarci yaransa su yi wa PDP aiki ne a zaben 2023

Rivers - Shugabannin jam’iyyar APC na neman tado tsohon rikicinsu a sakamakon ziyarar da su ka kai wa Abdullahi Umar Ganduje.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa bangarorin APC na reshen jihar Ribas sun ziyarci shugaban jam’iyya na kasa a sakatariya a Abuja.

‘Yan bangaren da ke tare da Nyesom Wike sun fadawa Dr. Abdullahi Umar Ganduje cewa Rotimi Amaechi ya goyi bayan PDP ne a 2023.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar ya zo bayan Bola Tinubu a 2023 Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Bola Tinubu ko Atiku Abubakar?

Kara karanta wannan

Atiku Ya Fadi Yadda Buhari Ya Durkusar da Kasuwancinsa Wajen Fallasa Tinubu

Kamar yadda rahoton ya bayyana, tsagin gwamnan sun ce tsohon ministan sufurin da mutanensa sun yi wa Alhaji Atiku Abubakar aiki ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An jefi Amaechi da zargin ganawa da Wazirin Adamawa kafin zaben shugaban kasa, sai ya umarci mutanensa su goyi bayan PDP a zabe.

Jagoran wannan tafiya, Tony Okocha ya yi ikirari a lokacin da shi da sauran shugabannin reshen Ribas su ka zauna da 'Yan APC NWC.

Kul aka ba 'Yan Amaechi mukami a APC

Ganin bai yi wa Bola Ahmed Tinubu kamfe ba, Okocha ya roki shugabannin APC su yi watsi da bangaren Amaechi wajen rabon mukamai.

Cif Okocha ya roki Ganduje da ya tuntubi Ministan birnin Abuja watau Nyesom Wike duk da ya na jam’iyyar PDP idan za a raba mukamai.

Jagororin na APC sun tuhumi Tony Cole, Dakuku Peterside, Chukwudi Dimkpa da sauran magoya bayan Amaechi da taimakawa Atiku.

Kara karanta wannan

Sunan Ministan Buhari Ya Fito Wajen Shari’a da Diezani Alison-Madueke a Kotu

Karyar banza ce Inji Amaechi

Mai magana da yawun Rotimi Amaechi watau Chukwuemeka Eze, ya shaidawa jaridar cewa zargin da ake yi bai da ko da kanshin gaskiya.

Cif Eze ya ce yunkuri ake yi na bata tsohon ministan, ya ce irinsu Okocha da Magnus Abe sun bar APC, sun raba gari da Amaechi a tafiyar siyasa.

Da ya tashi jawabi, Ganduje ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyar su daina hura wutan rikici.

Tinubu da takardar shaidar bogi

Bangaren Atiku Abubakar su na ikirarin Shugaban kasa ya gabatarwa INEC da diflomar bogi, rahoto ya zo cewa Bola Tinubu na cikin barazana.

Demola Olarewaju ya na cikin masu ganin kotun koli za ta tsige Bola Ahmed Tinubu tun da dokar kasa ta hana tsayawa takara da takardar karya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng