Farfesa Kperogi Ya Bayyana Cewa Tinubu Ya Yi Ganganci Wurin Satifiket Da Ya Mika INEC

Farfesa Kperogi Ya Bayyana Cewa Tinubu Ya Yi Ganganci Wurin Satifiket Da Ya Mika INEC

  • Mai fashin bakin siyasa, Farooq Kperogi ya bayyana cewa Tinubu ya yi ganganci da ya mika takardar Difloma ga hukumar zabe
  • Kperogi ya ce duk da ya ke hakan ba saba doka ya yi ba amma akwai ganganci idan aka duba yadda Najeriya ke daukar satifiket
  • A kwanakin baya, Farfesa Kperogi ya bayyana cewa Tinubu ya mallaki takardun bogi inda yanzu ya lashe amansa

Chicago, Amurka – Farfesa Farooq Kperogi ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi kuskure da ya mika takardun da wani ya buga masa ga hukumar zabe ta INEC.

Kperogi wanda dan Najeriya ne da ke zaune a Amurka ya ce Tinubu ya yi ganganci da ya mika kwafi wanda ba daga Jami’ar ta fito ba a 2022, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Dambarwar Satifiket: 'Dalilin Da Ya Sa Ba Za A Zargi Tinubu Da Laifi Ba', Farfesa Kperogi Ya Yi Bayani

Kperogi ya fadi satifiket da ya kamata Tinubu ya mika ga INEC
Farfesa Kperogi ya yi martani kan takardun Tinubu. Hoto: Bola Tinubu, INEC Nigeria.
Asali: Facebook

Meye Kperogi ya ce kan takardun Tinubu?

Farfesan ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya yi a yau Asabar 7 ga watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kuskure ne mutum ya ce Tinubu ya mika takardar bogi inda ya ce a Amurka satifiket ba shi da wani tasiri wurin kammala karatu.

Ya ce:

“Na yarda Tinubu ya yi ganganci, ya na Najeriya kasar da ke da manufa daban kan satifiket idan aka kwatanta da Amurka.
“Ya kamata ya mika kwafin takardar Difloma daga Jami’ar amma sai ya mika wani abu daban wanda ya yi kama da na Salisu Buhari.
“Bambancin da na Salisu Buhari wanda ya mika takardun bogi daga Jami’ar Toronto shi ne shi Salisu bai mallakesu ba, amma Tinubu ya halarci Jami’ar Chicago.”

Kperogi ya kara da cewa:

“Abin da Tinubu ya yi da satifiket na shi zai lalata masa siyasa a Najeriya amma ba laifi ba ne musamman a Amurka.”

Kara karanta wannan

Da Gaske Akwai Alamar ‘Mace’ a Takardun Jami’ar CSU – Lauyan Tinubu Ya Kawo Dalili

Farfesan a baya ya bayyana cewa Tinubu ya saba doka musamman wurin mika takardun karatunsa ga hukumar zabe ta INEC.

Amma sai ga shi yanzu ya yi amai ya lashe inda ya ce Tinubu bai saba wata doka ba musamman a Amurka.

Kperogi ya yi martani kan dambarwar takardun Tinubu

A wani labarin, Farfesa Farooq Kperogi ya bayyana cewa babu inda Shugaba Tinubu ya saba doka a maganar takardunshi.

Kperogi ya ce idan aka kwatanta da kasar Amurka, satifiket ba shi da wani tasiri kamar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.