Jigon Jam’iyya ya ce ba zai taba-goyon bayan ‘Dan takaran da APC ta tsaida ba

Jigon Jam’iyya ya ce ba zai taba-goyon bayan ‘Dan takaran da APC ta tsaida ba

  • Sanata Magnus Abe ya ce ba zai taba goyon bayan Tony Cole ya zama Gwamnan jihar Ribas ba
  • ‘Dan adawan na Rotimi Amaechi ya ce babu abin da Cole ya tsinanawa APC tun da aka kafa ta
  • Magnus Abe bai hakura da samun tikiti a APC ba, yana sa ran shi zai zama ‘Dan takara a 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Babban jigo na jam’iyyar APC a Ribas da yankin Neja-Delta, Magnus Abe, ya shaida cewa ba zai marawa takarar Tonye Cole baya a zabe mai zuwa ba.

Da aka yi hira ta musamman da shi a gidan talabijin Channels a ranar Talata, Magnus Abe ya nuna ya ja layi tsakaninsa da ‘dan takaran APC na Ribas.

Sanata Abe wanda shi ma yana son kujerar Gwamna tun ba yau ba, ya ce Cole bai kai matsayin da jam’iyyar APC za ta tsaida shi a matsayin ‘dan takararta ba.

Kara karanta wannan

Mawaki ya ji uwar bari, ya tona cewa kudi aka biya shi domin yi wa Bola Tinubu waka

Tsohon Sanatan na Gabashin Ribas a majalisar dattawa ya ce sanannen abu ne cewa bai tare da Cole, domin ‘dan takarar na su bai da abin da zai iya nunawa.

A tattaunawar da aka yi da shi a shirin siyasa na Political Paradigm a Channels TV, Abe ya ce ba zai sa wa APC hannu a zaben gwamna da za ayi a 2023 ba.

An raba jiha a Ribas

“A’a, ba zan goyi bayan Tonye Cole, ina tunanin kowa ya fahimci wannan.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Buhari a Fatakwal
Shugaban kasa a Jihar Ribas Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

“Babu hannu na a yadda ya zama ‘dan takara, a iyakar sani na, bai cikin jam’iyyar mu, kuma bai bada gudumuwa wajen kafa jam’iyyar ba.”
“A tarihi, babu abin da ya tabuka a jihar mu (Ribas).”

Wasu makudan kudi sun bace

“Akwai zargin da ake yi na cewa sama da Dala miliyan 55 na dukiyar jihar Ribas sun shiga asusunsa ta hannun wajen Rotimi Amaechi”

Kara karanta wannan

Babban Lauyan Najeriya ya raba gardama game da takarar Musulmi da Musulmi a APC

Abe yake cewa ana zargin an tafka wannan badakala ne a mulkin Rotimi Amaechi, Abe ya yi aiki a gwamanatin, amma ya wanke kan shi daga zargin badakalar.

Da aka yi zaben fitar da gwani a watan Mayu, Sanata Abe bai yi nasarar samun takarar gwamna ba, amma har yanzu yana sa ran shi zai rike tutar APC a 2023.

APC ta tsaida ‘Dan takara a Sokoto

Dazu aka ji labari ‘Dan takarar Gwamna a Sokoto, Ahmed Aliyu ya dauki Idris Muhammad Gobir ya zama ‘Dan takarar Mataimakin Gwamna a zaben 2023.

Baya ga Digiri shi da Idris Gobir ya ke da su, ya yi aiki Gwamnati, da a ofishin Ministan tarayya, kuma tsohon Kwamishina ne, har Kantoma ya rike a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng