Kuri’u Marasa Inganci Da Wasu Dalilai Da Suka Sa Kotun Zabe Tsige Gwamnoni 2 Cikin Watanni 5

Kuri’u Marasa Inganci Da Wasu Dalilai Da Suka Sa Kotun Zabe Tsige Gwamnoni 2 Cikin Watanni 5

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnoni na 2023 a jihohi 28 da aka gudanar da zaben ranar 18 ga watan Maris ta tsige akalla gwamnoni biyu cikin wata biyar da rantsar da su.

Dokar zaben Najeriya ta bayar da damar da fusatattun jam'iyyu za su shigar da kara a kan jam'iyyar da ta yi nasara cikin kwanaki 21, kuma ana sa ran kotunan zaben su saurari shari'ar tare da yanke hukuncinsu kan kararrakin cikin kwanaki 180.

Kotun zabe ta tsige gwamnoni biyu cikin watanni biyar
Kuri’u Marasa Inganci Da Wasu Dalilai Da Suka Sa Kotun Zabe Tsige Gwamnoni 2 Cikin Watanni 5 Hoto: Abdullahi Sule, Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Yayin da cikar wa'adin ke kara karatowa, kotunan zabe a jihohi biyu sun tsige gwamnoni. Ga jerin gwamnonin da aka tsige a kasa:

1. Abba Kabir Yusuf

Gwamnan jihar Kano wanda ya kasance dan jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) shine gwamna na farko da kotun saurararon kararrakin zaben gwamna ta tsige. Ta ayyana Nasir Gawuna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Zaben Kano: Abba Gida Gida Da Jam'iyyar NNPP Sun Sake Shiga Matsala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin da Mai shari'a Oluyemi Akintan-Osadebay ke shagoranta ya yanke cewa kuri'u 165,663 da gwamnan ya samu basa bisa ka'ida saboda ba a rattaba hannu a takardun zaben ba.

Bayan cire kuri'un da basu da amfani, kotun ta sanar da cewar Gawuna na APC ne ya lashe zaben gwamnan na ranar 18 ga watan Maris.

2. Abdullahi Sule

Hukumar zabe ta ayyana Gwamna Sule na jihar Nasarawa a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris a jihar, inda ya zarce a karo na biyu kwatsam sai kotun zabe ta tsige shi.

An tsige Gwamna Sule na APC kan hujjar cewa zaben da ya samar da shi bai bi ka'idar dokar zabe na 2022 ba, kuma cewa ba shine ainahin wanda ya lashe zaben ba.

Daga nan sai kotun zaben ta ayyana David Umbugadu na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin ainahin wanda ya lashe zaben yayin da ta bukaci hukumar INEC da ta janye takardar shaidar cin zabe da ta bai wa Gwamna Sule.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, kotun zaben ta saurari shari'ar akalla gwamnonin jihohi 19 tare da yanke hukunci a kansu.

Hukuncin kotun zaben gwamnan Kano: An shawarci jam'iyyar NNPP da ta tari zaben 2027

A wani labarin kuma, mun ji cewa biyo bayan hukuncin kotun zaben gwamnan jihar Kano, an bukaci jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da ta sake dabara sannan ta shirya ma zabe na gaba.

Kungiyar Stand Up Nigeria (SUN) ce ta yi wannan kira a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Asabar, 30 ga watan Satumba, rahoton The Cable.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng