Mambobin Jam'iyyun PDP Da Labour Dubu 50 Ne Su Ka Sauya Sheka Zuwa APC A Jihar Bayelsa

Mambobin Jam'iyyun PDP Da Labour Dubu 50 Ne Su Ka Sauya Sheka Zuwa APC A Jihar Bayelsa

  • Yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamna a jihar Bayelsa, lamarin na sake daukar hankali
  • A jiya Alhamis mutane sama da dubu 50 daga jam'iyyun PDP da Labour sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
  • Sun yi alkawarin hada karfi da karfe don tabbatar da samun nasara a zaben da za a gudanar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Bayelsa - Dubban magoya bayan jam'iyyun PDP da Labour ne su ka sauya sheka zuwa jam'iyya APC a jihar Bayelsa.

Akalla mutane dubu 50 a jiya Alhamis su ka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a jihar.

Mambobin PDP, Labour sun koma APC a jihar Bayelsa
APC A Jihar Bayelsa Ta Yi Babban Kamu. Hoto: Sylva, Douye Diri.
Asali: Facebook

Yaushe mambobin PDP, Labour su ka koma APC?

Wannan na zuwa ne yayin da ake daf da gudanar da zaben gwamna a watan Nuwamba mai zuwa, cewar TheCable.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Zaben Kaduna: Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Zaben Gwamna, Ta Fayyace Komai Na Rudani

An karbi sabbin 'yan jam'iyyar APC ne a jiya Alhamis 28 ga watan Satumba a Yenagoa yayin kamfe.

Dukkansu sun nuna goyon bayansu ga dan takarar gwamna a jam'iyyar APC, Timipre Sylva.

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa a yankin Arewa, Ali Dalori shi ya karbi sabbin tuban a jiya, Leadership ta tattaro.

Su waye a PDP, Labour su ka koma APC?

Tsoffin shugabannin kananan hukumomi a jihar, Victor Isaiah da Nathaniel Sylva da kuma Ebinyu Turner na daga cikin wadanda su ka sauya shekan.

Yayin da ya ke magana, Sylva ya ce za su hada kai da wadanda su ka sauya shekan don kawar da Gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP daga mulki.

Ya ce babu wata barazana da za ta hana shi da jam'iyyar APC lashe wannan zabe da za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Dan Takarar Gwamnan NNPP Ya Sauya Sheka Zuwa APC, Ganduje Ya Yi Shagube Ga Kwankwaso

"Babu wani abu da za mu bari wurin ganin mun lashe zaben gwamna a wannan jiha.
"Kuma babu wata barazana da za ta kashe mana gwiwa wurin ganin mun kifar da wannan gwamnati ta PDP a jihar Bayelsa."

A bangarenshi, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe kuma shugaban kwamitin kamfe na zaben ya ce za su hada karfi da karfe don ganin sun lashe zaben.

APC ta kaddamar da kwamitin kamfe a jihar Imo

A wani labarin, jam'iyya mai mulki ta APC ta kaddamar da kwamitin kamfe a jihar Imo.

Shugaban APC, Abdullahi Ganduje shi ya jagoranci tawagar inda ya yi alkawarin bai wa Gwamna Hope Uzodinma goyon baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel