Zaben Bayelsa: Wike Ya Bayyana Sharadinsa Kafin Ya Yarda Ya Yiwa PDP Aiki

Zaben Bayelsa: Wike Ya Bayyana Sharadinsa Kafin Ya Yarda Ya Yiwa PDP Aiki

  • Sabon ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana abin da dole sai jam'iyyarsa ta yi kafin ya mara mata baya
  • Wike a cikin wata tattaunawa ya bayyana cewa dole sai PDP ta nemi afuwarsa da wasu takwarorinsa kafin ya yi aiki tare da su a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa
  • Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya cika bakin cewa har yanzu yana nan daram a PDP kuma yana alfaharin yin aiki a ƙarƙashin Shugaba Tinubu

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa shugabannin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sai sun nemi afuwarsa da takwarorinsa kafin ya yi aiki tare da su a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa.

Wike ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da gidan talbijin na Channels tv a shirinsu na Politics Today a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-Jigan PDP Da Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Bai Mukami

Wike ya gayawa jam'iyyar PDP sharadinsa
Wike ya ce dole sai PDP ta nemi afuwarsa Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Da ya ke cigaba da magana, Wike ya bayyana cewa shugabannin jam'iyyar PDP akwai kura-kuran da dole sai sun gyara kafin ya duba yiwuwar yin aiki tare da su a zaɓen na ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya cika bakin cewa ya yi aikin da ya dace lokacin da ya ke gwamna, sannan bai damu da zagin da yaran Atiku ke yi masa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina alfahari da goyon bayan Tinubu", Wike

Wike ya kuma yi nuni da cewa yana alfahari cewa ya goyi bayan ɗan takarar da ya tsayawa gaskiya da adalci a lokacin zaɓen shugaban ƙasa, ta hanyar yaƙar rashin adalcin PDP.

"Akwai abubuwa da dama da dole sai sun gyara kafin na yarda na yi aiki da PDP. Suna sane cewa sai sun nemi afuwata da sauran takwarorina."

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Na Yi Mamaki Da Tinubu Ya Nada Ni Ministan Abuja, Wike

"Ina ganin ɗan takarar shugaban ƙasar da yaransa a talbijin kullum suna ɓaɓatu, sun tura su domin su zage ni, ban damu ba."
"Na bar jihata cike da farin ciki kamar wani jarumi. Na yi aiki domin samun adalci da gaskiya."
"Ba zai yiwu a sanya ni cikin kowacce irin tawaga ba, duk abin da na ke so na yi, zan yi. Idan ina son shiga APC, zan yi magana da mutane na."

Wike Ya Daga Yatsa Ga PDP

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya sake takalar fada tsakaninsa da jam'iyyar PDP.

Ministan na birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa babu wanda ya isa a jam'iyyar ya dakatar da shi ko ɗaukar matakin ladabtarwa a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng