Kano: Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Kori CMD Na Asibitin Hasiya Bayero

Kano: Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Kori CMD Na Asibitin Hasiya Bayero

  • Gwamnatin jihar Kano ta kori shugaban Asibitin yara Hasiya Bayero, Dakta Yunusa Sanusi, saboda rashin iya jagoranci
  • Hukumar kula da Asibitoci ta jihar (HMB) ta ce an ɗauki wannan matakin ne bayan dogoron nazari da tattaunawa da masu ruwa da tsaki
  • Ta kuma tura sabon CMD da kwararrun likitoci biyu domin tabbatar da komai ya tafi bisa tsarin gwamnati a Asibitin

Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta kori babban darektan asibitin yara na Hasiya Bayero, Dakta Yunusa Sunusi, makonni uku bayan sake buɗe Asibitin.

Daily Trust ta tattaro cewa gwamnatin Abba Gida-Gida ta ɗauki wannan matakin ne bisa zarginin rashin kwarewa wajen tabbatar da tsare-tsaren duba mara lafiya kyauta.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Kano: Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Kori CMD Na Asibitin Hasiya Bayero Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Mai magana da yawun hukumar kula da Asibitoci ta jihar Kano (HMB), Samira Sulaiman ce ta bayyana haka a wata sanarwa ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Gwamnan Arewa Ya Lale Kudi Sama da Biliyan Ɗaya Ya Siyo Motoci 10 Domin Taimaka Wa Talakawa

Ta ce a wani aikin kai ziyarar ba zata da hukumar ke yi kan Asibitin da ke ƙarƙashinta, ta dira Asibitin Hasiya Bayero kuma ta gano rashin cancantar Darektan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa gwamnati ta kori shugaban Asibitin?

Samira ta bayyana cewa bayan gano shugaban Asibitin ya gaza a jagorancin duba marasa lafiya, kwantar da su, da ba su magani kyauta, nan take hukumar ta kore shi daga aiki.

Sanarwan ta ce:

“An dauki matakin ne bayan doguwar tattaunawa da Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Yusuf Labaran da babban sakataren hukumar kula da asibitoci, Dakta Mansur Mudi Nagoda."
"Kuma hakan ya biyo bayan tabbatar da cewa shugaban Asibitin ba zai iya tsara ma'aikata da kuma aiwatar da kudirin gwamnati na duba mara lafiya, kwantar da su da magani kyauta ba."
"A lokuta da dama mai girwa gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara Asibitin mafi yawa da tsakar dare kuma ya tarad da abinda bai kamata ba, ya umarci a gyara amma har yanzu jiya iyau."

Kara karanta wannan

Halin kunci: Jama'a Sun Farmaki Rumbun Abinci A Wata Jiha, Sun Kwashe Kayan Abinci Na Miliyoyi

Ta ƙara da cewa shugaban hukumar ya koka kan gazawar Darektan Asibitin Hasiya Bayero wajen tafiyar da harkokin duba marasa lafiya duk ya kasance kwararren likitan yara.

Matakan gyaran da gwamnatin Kano ta ɗauka

Dakta Nagoda ya bayyana cewa bisa haka, hukumar HMb da ma'aikatar lafiya suka ga ya dace su tura Dakta Ibrahim Ibni Muhammad, wanda ya san harkar shugabanci kuma likitan yara ya maye gurbin.

Haka zalika an tura kwararrun Likitoci, Dakta Jamila Sani da Dakta Aisha Yahaya, domin su ci gaba da tafiyar da Asibitin, Vanguard ta tattaro.

Har Yanzu Rabiu Kwankwaso Na Nan a Jam'iyyar NNPP, Robert

A rahoton na daban kuma Jigon NNPP ya bayyana abinda doka ta tanada kan matakin dakatar da Rabiu Musa Kwankwaso.

Mai bada shawara kan harkokin shari'a na jam'iyyar NNPP ta ƙasa, Robert Hon, ya jaddada cewa kwamitin amintattu (BoT) bai da ƙarfin ikon dakatar da Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan

PSC: Shugaba Tinubu Ya Sallami Manyan Jami'ai DIG 4, Ya Naɗa Waɗanda Zasu Maye Gurbinsu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262