Gwamnatin Adamawa Ta Siyo Motocin Sama da Biliyan Don Tallafa Wa Talakawa

Gwamnatin Adamawa Ta Siyo Motocin Sama da Biliyan Don Tallafa Wa Talakawa

  • Gwamnatin Adamawa ta lale naira biliyan 1.06 ta siyo motocin Bas guda 10 domin agaza wa talakawa a fannin sufuri
  • Sakataren gwamnatin jihar (SSG), Alhaji Auwal Tukur, ya ce nan ba da jimawa ba motocin zasu hau titi su ci gaba da aiki
  • Ya kuma bayyana cewa sun karbi biliyan 2 daga cikin biliyan 5 da FG ta yanke bai wa kowace jiha domin rage wa mutane radaɗi

Adamawa state - Gwamnatin jihar Adamawa karkashin jagorancin gwamna Ahmadu Fintiri ta lale kuɗi sama da naira biliyan ɗaya ta siyo motocin Bas guda 10.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnatin ta cefano motocin a kan kuɗi naira biliyan 1.060 domin magance tsadar kuɗin sufurin da ake fama da shi bayan cire tallafin man fetur.

Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa.
Gwamnatin Adamawa Ta Siyo Motocin Sama da Biliyan Don Tallafa Wa Talakawa Hoto: Ahmadu Fintiri
Asali: Facebook

Shugaban kwamitin raba kayan tallafi domin rage zafi na Adamawa, Alhaji Auwal Tukur, shi ne ya bayyana haka ga 'yan jaridar ranar Litinin a Yola.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Jama'a Sun Farmaki Rumbun Abinci A Wata Jiha, Sun Kwashe Kayan Abinci Na Miliyoyi

Ya ce kowace motar Bas ɗaya ta kai naira miliyan 106, jumullar guda 10 da gwamnatin ta siyo sun lamushe kuɗi N1.06bn.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tukur wanda shi ne Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) ya ce motocin Bas din za su taimaka wajen magance kalubalen da ma’aikatan gwamnati, dalibai da sauran jama’a ke fuskanta wajen biyan kudin sufuri.

A cewarsa, motocin Bas din za su hau kan titi su fara aiki ba kama hannun yaro nan ba da daɗewa ba bayan kafa ofishin kula da su, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Adamawa ya karbi kuɗin tallafi daga FG

Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta karbi Naira biliyan 2 daga cikin Naira biliyan 5 da gwamnatin tarayya ta yanke bai wa kowace jiha na tallafi.

Sakataren ya ƙara da cewa tuni gwamnati ta sayi tirela 50 na shinkafa domin rabawa kowace gunduma a fadin kananan hukumomin jihar 21.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Kwastomomi Sun Rage Zuwa Gida Karuwai a Kano, Gidan Magajiya Ya Dauki Zafi

Ya ce za a hada kayayyakin ne a cikin buhuna masu nauyin kilogiram 25 domin rage yawaitar sayar da su a kasuwa, ya kara da cewa, “muna fatan za su iso zuwa ranar Talata."

"Shinkafa da masara za a sayar da su a kan farashi mai rahusa, inda za a rage farashin da mafi ƙaranci kashi 50 cikin ɗari."

Ba Da Jimawa Ba Za a Bayyana Obi a Matsayin Shugaban Kasa, Abure

A wani rahoton na daban Julius Abure ya bayyana wanda yake da tabbacin zai samu nasara a Kotun sauraron ƙorafin zaben shugaban ƙasa.

Shugaban LP na ƙasa ya ce Peter Obi na dab da ɗarewa kujera.lamba ɗaya a Najeriya da zaran Kotu ta yanke hukunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel