Kwanaki Kadan da Fara Aiki, Ana Cacar Baki Tsakanin Ministan Tinubu da Gwamna

Kwanaki Kadan da Fara Aiki, Ana Cacar Baki Tsakanin Ministan Tinubu da Gwamna

  • Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya maida martani ga Ministan labarai da wayar da kan al’umma
  • Muhammed Idris Malagi ya soki Gwamnan a kan yadda ya soki lamarin janye tallafin fetur da aka yi
  • Ministan ya yi kaca-kaca da Gwamnatin Edo, zargin da kwamishinan Obaseki ya musanya a raddinsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Edo - A ranar Lahadi, gwamnatin jihar Edo, ta yi wa Ministan labarai da wayar da kan al’umma, Muhammed Idris Malagi martani a kan kalamansa.

Tribune ta ce hakan ya biyo bayan jawabin da Ministan ya yi, ya na mai yi wa Godwin Obaseki raddi game da batun cire tallafin man fetur da aka yi.

Raddin gwamnan ya fito ta bakin Kwamishinan sadarwa da wayar da kan al’umma na jihar Edo, Chris Osa Nehikhare a karshen makon da ya wuce.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Gwamnan PDP Ya Fusata, Ya Kori Hadiman Mataimakin Gwamna Daga Aiki Kan Abu 1

Ministocin tarayya
Bola Tinubu ya rantsar da Ministoci Hoto: www.osgf.gov.ng
Asali: UGC

Cire tallafin fetur babu tsari a kasa

Mai girma Gwamnan Edo ya yi Allah-wadai da yadda gwamnatin Bola Tinubu ta tunkari matakin cire tallafin man fetur wanda ya jawo tsadar rayuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Chris Nehikhare yake cewa gwamnatin tarayya ta maimaita kuskuren da ta yi a lokacin da Obaseki ya koka game da tsarin canjin kudi da aka yi a 2022.

Kwamishinan yake cewa canza manyan takardun Naira da CBN ya yi ya kawowa gwamnati cikas, lamarin da ya jawo jama'a su rika kokawa a Najeriya.

Ana wahala a mulkin Tinubu

A jawabin da ya fitar kamar yadda rahoton ya bayyana, gwamnatin Edo ta ce ya kamata Muhammed Idris ya san wahalar da jama’a su ke sha a yau.

Tun daga lokacin da Bola Tinubu ya zama shugaban kasa, Nehikhare ya ce Obaseki ya na halartar taron NEC, akasin abin da ministan tarayyar ya fada.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Zaftare Yawan Jami'an Gwamnati Masu Fita Kasar Waje Saboda Rage Kashe Kudi

Har ila yau, kwamishinan sadarwan ya kuma ce zargin da gwamnatin Tinubu ta ke yi wa jihar Edo na rashin tabuka abubuwan kirki ba gaskiya ba ne.

"Gwamnatin jihar Edo ta na so ta nuna rashin jin dadinta a kan jawabin da ake cewa Ministan sadarwa da wayar da kai, Muhammad Idris ya yi a kan Gwamna Godwin Obaseki game da yadda Gwamnatin tarayya ta tankari abin da ya biyo bayan cire tallafin man fetur.
Abin takaici da bakin ciki ne yadda Gwamnatin Tarayya ta ke so ta rufewa al’umma baki da kuma zababben gwamna mai farin jini da yake fadawa masu mulki gaskiya a halin da mu ka samu kan mu."

- Chris Osa Nehikhare

Kukan Sheikh Shuaibu Salihu Zaria

Ana da labari Sheikh Shuaibu Salihu Zariya ya ankarar da Gwamnan Kaduna cewa wasu matan aure na wulakanta kan su domin su samu abinci.

Malamin addiin yake cewa magidanta su na gudu su na barin gidajensu saboda talauci. A dalilin haka ya roki shugabanni su tausayawa talaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel