Yadda Kawancen Kwankwaso-Tinubu Ya Wargaje, Ganduje Ya Dawo Cikin Lissafin Siyasa

Yadda Kawancen Kwankwaso-Tinubu Ya Wargaje, Ganduje Ya Dawo Cikin Lissafin Siyasa

  • NNNP ta zama jam’iyya mai mulki a jihar Kano a sakamakon doke Nasiru Gawuna da aka yi a zaben bana
  • Tsugune ba ta kare ba domin Abdullahi Umar Ganduje ya farfado da APC bayan zama shugaban jam’iyya
  • Tsohon Gwamnan na Kano ya na da wahalar fada a siyasa, Kwankwasiyya ta gagara kai shi kasa har gobe

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Zaman Abdullahi Umar Ganduje ya farfado da jam’iyyar APC a jihar Kano, masu nazarin siyasa sun lura abubuwa sun fara canza zani.

Kafin Bola Ahmed Tinubu ya shiga ofis, sai aka ji ya yi wata ganawar sirri da Rabiu Musa Kwankwaso a kasar waje, hakan ya fara hargitsa APC.

Da farko an yi tunanin gwamnatin Tinubu za ta jawo ‘yan adawa irinsu Rabiu Kwankwaso da ya yi takara a NNPP, a karshe aka yi watsi da su.

Kara karanta wannan

Makiya Kano Za Su yi Amfani da Kotu, A Tsige NNPP a Dawo da APC - Malamin Addinin Musulunci

Abdullahi Ganduje
Tsohon Gwamnan Kano ya zama Shugaban APC Hoto: Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Wasu su na zargin yadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya shiga yakar Abdullahi Ganduje daga shiga ofis ya bata alakar NNPP da APC a sama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabon Ministoci da Tinubu ya yi

A lokacin da sunayen ministoci ya fito, babu kowa daga bangaren Ganduje da kuma Kwankwasiyya, kwatsam sai aka ji a n cire sunan Maryam Shetty.

Wanda ta canji Shetty kuwa ita ce Dr. Mariya Mahmud Bunkure wanda ta yi kwamishina na shekaru hudu lokacin da Ganduje ya ke mulkin Kano.

Shari'ar zaben Gwamnan Kano

Yayin da jam’iyyar adawa mai alamar kayan marmari ta lashe zabe kuma ta shiga ofis, shari’ar da aka yi a kotun zaben gwamnan Kano ya tada hankalinta.

Kafin yanzu, lauyan NNPP ya shaida mana ba su shakkar yin nasara a kotu, amma alamu ya nuna cikin magoya bayan Kwankwasiyya ya duri ruwa a yau.

Kara karanta wannan

Aiki ya fara: Daga zuwa, Ganduje ya yi sabbin nade-nade a kwamitin NWC na APC

Wadannan abubuwa duk sun faru ne bayan APC ta nada Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyya, ya canji Abdullahi Adamu da ya yi murabus.

Labari ya canzawa APC a Agusta

A sakamakon mukamin da Ganduje ya samu a Agusta, APC ta dunkule a jihar Kano, sannan wasu daga cikin ‘ya ‘yanta sun fara samun mukamai daga Abuja.

Duk da APC ta rasa mulki da rinjayen ‘yan majalisu, ana ganin magana za ta iya canza a kotun zabe kamar yadda aka gani a shari’ar ‘dan majalisar Tarauni.

Muhuyi Rimin Gado v Ganduje

Baya ga haka, reshe ya juye da mujiya da Muhuyi Rimin Gado mai kokarin binciken Abdullahi Ganduje a kan zargin badakalar fai-fen karbar rashawa.

A jiya aka samu labari cewa hukumar EFCC ta kasa da kan ta, ta bayyana cewa ta neman shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng