Ministoci: An Alakanta Ganduje Da Cire Sunan Maryam Shetty Daga Cikin Wadanda Tinubu Zai Nada

Ministoci: An Alakanta Ganduje Da Cire Sunan Maryam Shetty Daga Cikin Wadanda Tinubu Zai Nada

  • Tinubu ya sanar da maye sunan Maryam Shetty da na Mariya Bunkure cikin waɗanda zai ba minista
  • Ba a ba da wani dalili ba kan cire sunan fitacciyar 'yar jam'iyyar ta APC daga jihar Kano
  • Maryam Shetty dai ta samu labarin cewa an zare sunan na ta ne a lokacin da ta isa zauren Majalisar Dattawa da nufin a tantance ta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Wani sabon rahoto ya nuna cewa an cire sunan Maryam Shetty daga cikin ministocin da Tinubu zai nada ne saboda ba ta cikin tafiyar siyasar Ganduje.

Ganduje dai shi ne tsohon gwamnan Kano, kuma sabon shugaban jam'iyyar APC mai mulki da aka zaba kwanan nan.

An bayyana dalilin cire sunan Maryam Shetty
An alaƙanta Ganduje da sanya hannu wajen cire sunan Maryam Shetty. Hoto: @MaryamShetty_ @officialABAT
Asali: Twitter

Sunayen ministoci: An maye sunan Maryam Shetty da abokiyar karatunta, Mariya Mahmoud Bunkure

Kara karanta wannan

Jerin Ministoci: Dalilin Da Yasa Tinubu Ya Maye Gurbin Maryam Shetti Da Abokiyar Karatunta Mariya Mahmoud

Wata majiya ta kusa da Ganduje ta shaidawa Daily Trust cewa, an maye sunan Maryam Shetty da na abokiyar karatunta, Dakta Mariya Mahmoud Bunkure saboda ita ba gidan siyasar Ganduje take ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dakta Mariya Bunkure dai tsohuwar kwamishiniyar ilimin manyan makarantu ce a lokacin Abdullahi Ganduje.

Majiyar ta kara da cewa, karin wani dalili da ya sa aka cire sunan Maryam Shetty shi ne, saboda caccakar wasu tsare-tsare da Ganduje ya zo da su a can baya da ta yi.

Daga ciki akwai magana da ta yi a kafafen sada zumunta dangane da cire Sarkin Kano Muhammad Sanusi II da aka yi daga sarauta.

A wani rahoto da jaridar Leadership ta yi, an bayyana Maryam Shetty a matsayin mace mai son taimakon matasa da kuma son ci gabansu.

Kara karanta wannan

Kano: Muhimman Abubuwa 5 Da Ba Ku Sani Ba Game Da Maryam Shetty Da Tinubu Ya Sauya Sunanta A Jerin Ministoci

Bada sunan jikar sarkin Kano matsayin minista ya janyo cece-kuce

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan cece-kucen da jama'a suka sha musamman a kafafen sada zumunta, biyo bayan bayyana sunan Maryam Shetty a matsayin minista daga Kano.

An bayyana cewa Maryam Shetty ta kasance cikin 'yan matan da jam'iyyar APC ke ji da su a ƙasa baki ɗaya.

Wasu sun yi ƙorafin cewa ba ita ce ta fi dacewa da matsayin ministar da ke wakiltar jihar Kano ba.

Mutane sun caccaki sanya Bello Matawalle cikin ministocin da Tinubu zai naɗa a gwamnatinsa

Legit.ng a baya ta kawo muku cece-kucen da jama'a suka yi dangane da bayyana sunan Bello Matawalle da aka yi cikin waɗanda Tinubu zai ba minista.

Wasu na ganin cewa bai cancanta ba duk kuwa da irin muƙaman da ya riƙe a baya kafin zamansa gwamnan jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng