Abba Ya Jawo Kwankwaso Ya Gagara Zama Ministan Bola Tinubu, Jam’iyyar APC

Abba Ya Jawo Kwankwaso Ya Gagara Zama Ministan Bola Tinubu, Jam’iyyar APC

  • Rabiu Musa Kwankwaso da mutanensa ba su iya samun mukami a gwamnatin APC mai-mulkin Najeriya ba
  • Jagora kuma Darektan yada labarai na jam’iyyar APC ya na ganin akwai laifin gwamnatin Abba Kabir Yusuf
  • Bala Ibrahim ya ce ganin abin da Abba Gida Gida yake yi wa Abdullahi Ganduje ne Bola Tinubu ya canza shawara

Abuja - Jam’iyyar APC ta na ganin yawan sukar Abdullahi Umar Ganduje da ayyukansa ya cuci Rabiu Musa Kwankwaso wajen nada ministoci.

Darektan yada labarai na APC, Bala Ibrahim ya zanta da Punch, ya shaidawa jaridar gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta hana a tafi da Rabiu Kwankwaso.

Da farko an yi tunanin Rabiu Musa Kwankwaso ya na da wuri a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, ganin yadda su ka rika yin zama a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Ke Jawo Mataimakan Gwamna Su Yi Fada da Gwamnoni a Jihohi – Ganduje

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

NNPP ta hana Ganduje sakat

Ganin yadda sabuwar gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta taso Abdullahi Ganduje a gaba a Kano, Bala Ibrahim ya ce hakan ya canza lissafin siyasar kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana ganin Gwamna Abba wanda aka fi sani da Abba Gida Gida, ya yi nasara a NNPP a zaben jihar Kano ne sakamakon farin jin jagoran Kwankwasiyya.

Ganduje ya fi Kwankwaso amfani a siyasa

"Kwankwaso ba abin wasa ba ne a siyasar Kano. Amma yadda ‘Yan Kwankwasiyya suka rika yi, ya jawo goyon bayan Kwankwaso ya yi kasa.
Wannan kuwa saboda hayaniyar da tafiyar ta ke kawowa a Kano da ma Najeriya.
Dole shugaban kasar ya duba yadda ake ciki, ya auna nauyin siyasa da aiwatar da manufofinsa, musamman ganin ya samu goyon bayan Kanawa.
Babu yadda za ka yi watsi da gawurtar Abdullahi Ganduje da kwarewarsa da gogewa idan aka zo maganar yadda ya ke buga siyasa a jihar Kano.

Kara karanta wannan

'Sabon Gwamna Sabon Sarki,' ‘Yan Sanda Sun Cafke Masu Rokon a Tunbuke Sarkin Kano

Idan aka daura su biyun a mizani mai kyau, nauyin Dr. Abdullahi Umar Ganduje a siyasa ya zarce na Rabiu Musa Kwankwaso nesa ba kusa.
Na yi imani shugaban kasa ya saurari mutanen da za su ba shi shawarar kwarai na gaskiya, wadanda su ke duba yanayin siyasar Jihar Kano.

- Bala Ibrahim

'Dan siyasar ya kara da cewa abin da Bola Tinubu ya duba kenan, sai bai yi wasa da Ganduje ba.

Rikici ya kunno cikin tafiyar NNPP

Wasu shugabanni a NNPP sun zargi Rabiu Kwankwaso da hada-kai da Bola Ahmed Tinubu yayin da aka ji labari jam'iyyar ta na zarginsu da zagon-kasa.

Kwamred Sunday Oginni yana so ‘Dan takaransu na 2023 ya rufawa kan shi asiri ya bar jam’iyyar ko dai kore shi saboda zargin ya yi wa APC aiki a zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel