Gwamnatin Tinubu Ta Dauko Tsofaffin Gwamnonin APC, Ta Hada Su da Muhimmin Aiki

Gwamnatin Tinubu Ta Dauko Tsofaffin Gwamnonin APC, Ta Hada Su da Muhimmin Aiki

  • Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta na kokarin ganin yadda za ta nada mukamai a gwamnatin Najeriya
  • A matsayinsa na Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya shaida haka a shafinsa na Twitter
  • Sanata Akume ya yi bayanin yadda aka daura nauyin hakan ga Badaru Abubakar da Atiku Bagudu

Abuja - A shirye-shiryen da ake yi ta bayan fage, Bola Ahmed Tinubu ya na so ya zakulo wadanda za su cike guraben mukamai a gwamnati.

Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume a wani jawabi da ya fitar a Twitter, ya nuna ana shirin nada mukaman da ke gwamnatin tarayya.

Gwamnati mai ci ta ruguza shugabannin majalisun sa ido a ayyukan gwamnatin tarayya, ana neman wadanda za su rike wadannan mukamai.

Gwamnatin Tinubu
Sakataren gwamnatin Tinubu, George Akume, Atiku Bagudu da Badaru Abubakar Hoto:@SGFAkume
Asali: Twitter

Ministocin gobe a kwamitin SGF

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Soke Lasisin Makarantu Masu Zaman Kansu Gaba Daya a Kano

Sanata Akume wanda ya shiga ofis a Yuni, ya ce kwamiti na musamman aka samar da zai taimaka wajen nemo wadanda za a ba mukaman nan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alhaji Badaru Abubakar da Muhammad Atiku Bagudu wanda sun yi gwamna a Jigawa da Kebbi tsakanin 2015 da 2023 za su jagoranci aikin.

"A bayan fage, ana aikin kawo sauyi wajen tabbatar da an samu cikakken tarin jama’a da za a kara taimakawa jami’an gwamnatin tarayya.
Sakamakon ruguza majalisun da ke lura da hukumomin gwamnatin tarayya, na kafa kwamiti da zai ba ni shawara wajen nada wadanda su ka cancanta a wadannan majalisu.
Kwamitin nan ya na karkashin jagorancin Muhammad Badaru Abubakar da Atiku Bagudu Abubakar.
Za su duba kwarewa da takardun fitattun mutane da su ka kware a fadin kasar nan. Wadannan mutane za su yi jagoranci da nuna inda za a dosa a majalisun, su taimakawa shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa Sun Mika Ta’aziyyarsu Ga Masarautar Zazzau Kan Rushewar Masallaci Da Ya Yi Sanadiyar Rasa Rayuka

A dalilin haka ne na hadu da jagororin nan domin duba aikin da kwamitin ya yi kuma mu daidaita ayyukan.
A karshe Gwamnatinmu ta kafu kuma wadannan majalisu su ne ragowar abin da ya ragewa Shugaba Asiwaju ya samar a ofis."

- George Akume

George Akume ya gaji Boss Gida Mustapha

An yi wannan ne kwanaki kadan bayan Boss Gida Mustapha, CFR ya yi ban-kwana da aiki.

Kwanaki kusan biyu da hawa mulki, aka ji Bola Ahmed Tinubu ya dauko kwararren ‘dan siyasa, George Akume ya zama sakataren gwamnatin tarayya.

Akume wanda ya yi mulkin Jiha, ya yi Sanata a Majalisar Dattawa, sannan ya yi shekaru hudu yana Minista a lokacin mulkin Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng