Tinubu Ya Tsige Duk Masu Kula da Hukumomi, Cibiyoyi da Kamfanonin Gwamnati

Tinubu Ya Tsige Duk Masu Kula da Hukumomi, Cibiyoyi da Kamfanonin Gwamnati

  • Bola Ahmed Tinubu ya bada dama a soke majalisun da ke lura da sa ido wajen ayyukan gwamnati
  • An tsige duka shugabannin da ke kula da ayyukan hukumomi, cibiyoyi da kamfanonin tarayya
  • Da zarar bukata ta tashi, ma’aikatun za su rubuta takarda ne kai tsaye zuwa ga Sakataren gwamnati

Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya amince a ruguza daukacin shugabannin majalisun da ke kula da ayyukan ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Tashar talabijin ta kasa ta ce umarnin shugaban kasar ya shafi ma’aikatu, cibiyoyi, hukumomi da uk wani kamfanin gwamnatin tarayya da ke Najeriya.

Hakan ya na zuwa ne jim kadan bayan Bola Tinubu ya kora hafsoshin tsaro da kwastam.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a wani taro: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, jawabin ya fito a ranar Litinin ta bakin Willie Bassey wanda shi ne Darektan yada labarai na sakataren gwamnati.

Kara karanta wannan

IMF Tayi Alkawarin Taimakon Najeriya Ganin Gyare-Gyaren da Bola Tinubu Ya Kinkimo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai wadanda abin bai shafa ba?

Ruguje shugabannin da aka yi bai shafin wasu ma’aikatu da hukumomin da ba su cikin karkashin sashe na 153 (i) na kundin tsarin mulkin kasa na 1999 ba.

Sanarwar ta shaida cewa wadanda abin ya shafa za su tattara su bar ofis ba tare da bata lokaci ba. Punch ta ce irinsu INEC, FCC, CCB, RMFAC da PSC sun tsira.

Idan ana neman sa hannu fa?

Idan akwai bukatar wani aikin da ya shafi sa hannun majalisun sa-idon da aka rusa, sanarwar ta umarci hukumomin su kai maganar zuwa ma’aikatunsu.

Wadanda su ke a matsayin Minitoci a yau za su dauki mataki a madadin majalisar. Hukumomin nan za su aika takardunsu ta karkashin manyan Sakatarori.

Su kuma Sakatarori za su gabatar da bukatun hukumomi, cibiyoyi, ma’aikatu ko kamfanonin zuwa ga shugaban kasa ta ofishin sakataren gwamnatin kasa.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban Kasa Tinubu Ya Girgiza Najeriya Cikin Makonsa Na 3 a Matsayin Shugaban Najeriya

Tribune ta ce wannan umarni ya fara aiki tun daga Juma’a da ta wuce, 16 ga watan Yuni 2023. An umarci ma’aikatan gwamnati su yi cikakkiyar biyayya.

An nada sababbin Masu bada shawara

Hadiza Bala Usman da Hannatu Musa Musawa sun samu shiga gwamnati. A yammmacin Litinin aka ji labari an ba su mukamai a mulkin Bola Tinubu.

Matan biyu sun fito daga jihar Katsina ne, Hadiza Usman ta rike mukamai a gwamnatin Nasir El-Rufai har daga baya ta zama shugabar hukumar NPA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng