Boss Mustapha Ya Mika Muhimman Takardu Na Ofishin SGF Ga Gorge Akume

Boss Mustapha Ya Mika Muhimman Takardu Na Ofishin SGF Ga Gorge Akume

  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, CFR, ya mika mulki ga magajinsa George Akume
  • Boss Mustapha, ya kuma mika muhimman takardu na ofishin SGF ga Akume bayan Tinubu ya rantsar da shi
  • Kafin nada shi a matsayin SGF, Akume ya kasance tsohon ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF) wanda ya yi aiki karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Boss Mustapha, ya sauka daga kujerarsa a ranar Laraba, 7 ga watan Yuni.

Boss Mustapha ya sauka sannan ya mika takardun ofishinsa ga magajinsa, George Akume, sabon sakataren gwamnatin tarayya.

Boss Mustapha yana mika shugabanci ga George Akume
Boss Mustapha Ya Mika Muhimman Takardu Na Ofishin SGF Ga Gorge Akume Hoto: Solomon Odeniyi
Asali: Facebook

Boss Mustapha ya mika takardu ga George Akume

Bikin mika mulkin ya gudana ne a ofishin SGF da ke Three Arms Zone a Abuja, jim kadan bayan isowar Akume, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan awanni bayan nan, sai shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Akume a kan kujerar.

"SGF aiki ne mai tsauri", Inji Bosss Mustapha

A halin da ake ciki, Mustapha ya bayyana cewa aikin sakataren gwamnatin tarayya mai wahala ne.

A cewar jaridar The Cable, Mustapha ya yi magana ne bayan rantsar da George Akume a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayya a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Laraba.

Mustapha ya shawarci Akume da ya shirya ma kalubalen da ke gabansa.

Yadda Tinubu ya kaucewa wuka mai guba yayin nada sakataren gwamnatin tarayya, Shehu Sani

A wani labari na daban, mun ji cewa Sanata Shehu Sani, ya yi shagube ga wani mai biyayya ga shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu bayan nada George Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku Ya Lissafa Jerin Mukamai 5 Da Bai Kamata Shugaban Kasa Tinubu Ya Ba Yan Siyasa Ba

Tsohon sanatan na Kaduna ya bayyana cewa sabon shugaban kasar ya yi dabara da ya kaucewa wuka mai guba ta hanyar zabar tsohon kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma'aikatansa da Sanata Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.

A cewarsa, da ace Tinubu ya zabi wani dan siyasa da ya ambata da sunan 'dan bani na iya' toh da ya haifar da rashin jituwa tsakaninsa (Tinubu) da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima. Cewa wannan mutumin zai dunga daukar kansa kamar ya fi su muhimmanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel