Tinubu Na Ganawa Da El-Rufai Da Wike a Fadar Gwamnatin Tarayya

Tinubu Na Ganawa Da El-Rufai Da Wike a Fadar Gwamnatin Tarayya

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya shiga wata ganawa da Shugaba Tinubu
  • Majiya mai ƙarfi ta tabbatar da cewa ganawar ba za ta rasa nasaba da batun tabbatar da El-Rufai matsayin minista ba
  • Majalisar Dattawa ta ƙi tabbatar da El-Rufai matsayin minista biyo bayan korafe-korafe da aka shigar a kansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Bayanan da ke fitowa na nuni da cewa Shugaba Bola Tinubu ya shiga gani da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Jaridar Vanguard ta ce bayan El-Rufai a wajen ganin, akwai tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

An tattauna batun muƙamin minista na El-Rufai

Wike na cikin mutane 45 cikin 48 da Majalisar Dattawa ta tabbatar a matsayin ministoci a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Sai dai Majalisar Dattawan ta ƙi yarda ta tabbatar da Malam Nasir El-Rufai saboda ƙorafe-ƙorafe da wasu daga cikin sanatocin suka shigar a kansa kan dalilai na tsaro.

Kara karanta wannan

Bidiyon Akpabio Yana Sanar Da Cewa An Tura Wa Yan Majalisa Kudaden Shakatawa Yayin Hutu Ya Janyo Cece-Kuce

Majiya mai ƙarfi ta ce wannan ganawar ba za ta rasa nasaba da ƙoƙarin da Tinubu yake yi ba na ganin Majalisar Dattawa ta tabbatar da El-Rufai a matsayin minista.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyar ta ƙara da cewa ba a lokaci guda Wike da El-Rufai suka iso fadar shugaban ƙasar ba, sun iso ne daban-daban.

An samu hargitsi wajen tantance ministan Tinubu

A wani rahoto da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa an samu hayaniya a zauren Majalisar Dattawan Najeriya yayin tantance Festus Keyamo domin ya zama minista a gwamnatin Tinubu.

Wani daga cikin sanatocin mai suna Sanata Nwokocha ne ya nemi majalisar ta dakatar da tantancewar da za ta yi wa Keyamo matsayin minista daga jihar Delta.

Sanatan dai ya zargi Keyamo da aikatawa Majalisar Dattawan wasu laifuka a can baya.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Bayan Tabbatar Da Mutane 45 Da Majalisar Dattawa Ta Yi, An Bayyana Mataki Na Gaba

Majalisa ta miƙawa Tinubu sunayen ministoci 45 da ta tabbatar

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan miƙa sunayen ministoci 45 da aka tabbatar da Majalisar Dattawa ta yi ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Mai taiamakawa Shugaba Bila Tinubu kan harkokin Majalisar Dattawa, Abdullahi Gumel ne ya bayyana hakan ranar Talata, 8 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng