Majalisar Malamai A Kaduna Ta Gargadi Sanatoci Da Su Yi Gaggawar Tabbatar Da El-Rufai A Matsayin Minista

Majalisar Malamai A Kaduna Ta Gargadi Sanatoci Da Su Yi Gaggawar Tabbatar Da El-Rufai A Matsayin Minista

  • Majalisar malamai a jihar Kaduna ta bukaci majalisar Dattawa da ta tabbatar da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai a matsayin minista
  • Sun bayyana cewa ba za su lamunci cin mutunci da kuma siyasar daukar fansa ba a kan tsohon gwamnan wanda ya ba da gudumawa sosai a zabe
  • Idan ba a mantaba a ranar Litinin 7 ga watan Agusta ne majalisar Dattawa ta ki tabbatar da Nasir El-Rufai da wasu mutane uku a matsayin ministoci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna – Majalisar malamai a jihar Kaduna ta soki dalilin da ya sa majalisar Dattawa ta ki tabbatar da tsohon gwamna Nasir El-Rufai a matsayin minista.

Majalisar a ranar Litinin 7 ga watan Agusta ta dakatar da tabbatar da tsohon gwamnan da wasu mutane biyu kan korafe-korafen tsaro, Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Tsohon Na Hannun Daman Peter Obi Ya Roki Majalisa Ta Tantance El-Rufai

Majalisar malamai ta gargadi sanatoci saboda kin tabbatar da Nasir El-Rufai a matsayin minsta
Majalisar Malamai A Kaduna Ta Koka Kan Shirin Da Wasu Ke Yi Game Da El-Rufai. Hoto: The Senate President.
Asali: Facebook

Meye majalisar ta ce kan sanatocin?

Majalisar malamai ta bayyana matakin sanatocin da wani salo na daukar fansa a kan tsohon gwamnan da kuma yin karan tsaye ga dokoki, Channels TV ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mataimakin shugaban majalisar malaman, Imam Muhammad Kassim ya ce zanga-zangar da ‘yan Shi’a suka yi a majalisar don nuna adawa da tabbatar da El-Rufai ba zai haifar da ‘da mai ido ba.

Meye asalin matsalar da majalisar ta ce?

Malaman suka ce wasu mutane ne da suka tsorata bayan an saka sunan El-Rufai a jerin ministocin ke son kawo cikas ga tabbatar da shi.

Sun bukaci majalisar Dattawa da ta gaggauta tabbatar da shi duba da irin gudumawar da ya bayar ga jam’iyyar APC a zaben da ya gabata.

Sun kara da cewa ‘yan Najeriya ba za su lamunci siyasar daukar fansa da kuma yin karan tsaye ga dokokin kasa ko jam’iyya ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da El-Rufai Da Wike a Gidan Gwamnati

Majalisa Ta Ki Tabbatar Da El-Rufai A Matsayin Minista

A wani labarin, majalisar Dattawa ta ki tabbatar da tsohon gwamna jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin minista a ranar 7 ga watan Agusta.

Hakan na zuwa ne bayan majalisar ta ce akwai korafe-korafe da suka shafi harkar tsaro a kan tsohon gwamnan da wasu mutane uku.

Sauran sun hada da Sanata Abubakar Danladi daga jihar Taraba da kuma Stella Oketete daga jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.