Shugaba Tinubu Na Gana Wa Shugabannin Ƙungiyoyin Kwadago a Villa

Shugaba Tinubu Na Gana Wa Shugabannin Ƙungiyoyin Kwadago a Villa

  • Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin ƙungiyoyin kwadago a fadar shugaban ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja
  • Wannan gana wa na zuwa ne a daidai lokacin da NLC da TUC suka jagoranci fara zanga-zanga a sassan Najeriya ranar Laraba
  • A cewar jagororin yan kwadagon, shugaba Tinubu ya kama hanyar magance buƙatunsu, kuma zasu koma su gaya wa sauran mambobinsu

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na gana wa yanzu haka da shugabannin ƙungiyoyin kwadugo na ƙasa a fadar shugaban ƙasa da ke birnin Abuja.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa waɗanda suka halarci taron daga bangaren 'yan kwadago sun ƙunshi shugaban ƙungiyar kwadago (NLC), Joe Ajaero, da shugaban ƙungiyar 'yan kasuwa (TUC), Festus Osifo.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu tare da shugabannin kwadago.
Shugaba Tinubu Na Gana Wa Shugabannin Ƙungiyoyin Kwadugo a Villa Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

NLC da TUC da sauran kwayensu sun tsunduma zanga-zanga yau Laraba, 2 ga watan Agusta a sassan Najeriya kan wahalhalun da aka shiga sakamakon cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: "Ko Kobo Ba'a Ceto Ba" NLC Ta Maida Martani Mai Zafi Kan Kalaman Shugaba Tinubu

Rahoton The Cable ya tattaro cewa zanga-zangar wadda NLC da TUC suka fara, ta nuna damuwa game da illar tsadar rayuwa ga ‘yan kasa, musamman masu rauni.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Menene maƙasudin wannan taro ana tsaka da zanga-zanga?

Kafar Channels tv ta kawo a rahotonta cewa shugabannin ƙungiyoyin sun bar fadar shugaban ƙasa mintuna 30 bayan shiga ganawa da shugaba Tinubu da ƙarfe 5:38 na yamma.

Da su ke tsokaci kan zaman, shugabannin kwadago sun bayyana cewa shugaban ƙasa ya ɗauƙi wasu alƙawurra na magance muhimman batutuwan da suka addabi al'umma.

Sun ƙara da bayanin cewa zasu koma su gabatar da rahoton wannan zama ga majalisar zartarwan ƙungiyoyinsu, a cewarsu a nan ne zasu ɗauki matsaya kan zanga-zangar da ke gudana.

Bugu da ƙari, sun sanar da cewa ƙungiyar kwadago zata gudanar da taron majalisar zatarwa ta ƙasa (NEC) ranar Alhamis, 3 ga watan Yuli, inda za su ƙara nazari kan batun.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Dauki Mataki Bayan Masu Zanga-Zanga Sun Kutsa Kai Cikin Harabarta Da Karfin Tuwo

Tinubu Ya Nada Atiku, Lalong, Matawalle a Karin Ministoci 19

A wani rahoton kuma kun ji cewa shugaba Tinubu ya aika sunayen ministoci rukuni na biyu ga majalisar dattawan Najeriya.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karanto karin Ministocin da ake sa ran za a nada bayan an tantance su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel