Gwamna Uba Sani Ya Sadaukar Da Kashi 50 Na Albashinsa Don Hidimtawa Talakawan Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Sadaukar Da Kashi 50 Na Albashinsa Don Hidimtawa Talakawan Kaduna

  • Sanata Uba Sani, gwamnan jihar Kaduna ya yafe rabin albashinsa inda ya umurci a yi amfani da kudin don hidimtawa talakawa da
  • Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya ce tuni an yi nisa game da batun kafa gidauniya ta musamman da za dora wa alhakin rage wa talakawa radadin zafin rayuwa a jihar
  • Sani ya sanar da hakan ne yayin rantsar da kwamishinoni a Kaduna inda ya gargade su da cewa duk wanda ya gaza sauke nauyin da aka dora masa za a sallame shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya sadaukar da kashi 50 na albashinsa ga wata gidauniya ta musamman domin talakawa, marasa galihu da gajiyayyu a jihar Kaduna.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli yayin rantsar da kwamishinoninsa 14 bayan Majalisar Dokokin Jihar ta tantance su.

Kara karanta wannan

An Samu Gwamnan APC Ya Yi Magana Game da Ministocin da Tinubu Ya Dauko

Gwamna Sani ya sadaukar da rabin albashinsa don tallafawa talakawan Kaduna
Uba Sani ya sadaukar da kashi 50 na albashinsa ya ce a yi amfani da shi wurin yi wa talakawa da marasa galihu aiki. Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Ya yi bayanin cewa tuni an yi nisa kan shirin kaddamar da gidauniyar ta talakawa da marasa galihu a yayin da ake kafa kwamitin da za ta jagoranci aiwatar da tsarin, rahoton Blue Print.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan ya ce:

"Za a kafa kwamiti na musamman don bullo da hanyar kafa gidauniya ta musamman, yana mai bada tabbacin zai sadaukar da kashi 50 na albashinsa."

Ya kara da cewa:

"Hakan na cikin sadaukarwa a bangarensa don rage kashe kudaden gudanar da ayyukan gwamnati a jihar, da gina rayuwar talakawa, marasa galihu da masu rauni, bisa tsarin 'Sustain Agenda'."
Bikin rantsarwa wacce mutane da dama suka halarta, a cewar gwamnan, "muhimmin mataki ne a tafiyar gwamnatinmu. An duba cancanta da kwarewa da ayyuka na baya ne wurin nada mukaman tare da kishin yi wa jihar Kaduna hidima."

Kara karanta wannan

Yadda Marigayi Albani Ya Hango Janye Tallafin Man Fetur Shekaru 9 da Suka Wuce

Lokaci ne na zage damtse a yi aiki, Gwamna Uba Sani ya fada wa kwamishinoni

Gwamna Sani ya tunatar da kwamishinonin an nada su mukami ne a lokaci da ake fuskantar kallubalen tattalin arziki a kasar don haka ya sa Shugaba Bola Tinubu ya dauki matakin cire tallafin mai.

Wani sashi na jawabinsa:

"Wannan lokaci ne na zage damtse. Dole mu dauki matakai na rage kudin gudanar da gwamnati a Kaduna. A matsayin mu na yan siyasa, dole mu nuna wa al'ummarmu misali. Mu kaucewa rayuwar facaka da almubazaranci. Ba zai yi wu mu rika fada wa mutane su yi sadaukarwa ba yayin da muke rayuwa ta walwala."
"Mun fara aiwatar da abin da muke fada a jihar Kaduna. Zan cigaba da amfani da tsaffin motoccin da na gada daga magabatana a jihar Kaduna. Dole dukkan kwamishinoni su yi amfani da tsaffin motocci. Dole mu yi sadaukarwar tare. Idan muka yi jagoranci a hakan, mutanenmu za su bi mu kuma su mara mana baya."

Kara karanta wannan

Tsumagiyar Tallafin Fetur Ta Bugi Gwamnoni, Ana Tunanin Rage Facakar Kudi

Za mu kori duk wani kwamishina da ya gaza, Gwamna Uba Sani

Ya kuma gargadi kwamishinonin cewa su tashi tsaye su magance kallubalen da ke gabansu domin ba za a amince da lalaci da rashin iya aiki ba.

"Ba za mu lamunci uzuri na rashin aiki ba. A jiharmu, dole mu ajiye abota a gefe.
"Za mu saka ido a kansu sosai (kwamishinonin) bisa alkalluman yin ayyuka. Duk wanda ya gaza za a sallame shi."

Gwamna Uba Sani, amma, ya bada tabbacin za a basu kayan aiki da goyon baya da suke bukata don yin ayyukansu yadda ya dace.

Gwamna Sani ya yi sabbin nade-nade a Kaduna

A wani rahoton kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya nada manyan masu ba shi shawara na musamman da hadimai.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a sahihin shafinsa na Twitter mai dauke da sa hannun sakataren watsa labaransa, Muhammad Lawal Shehu.

Kara karanta wannan

"Abin Ya Fara Isa Ga Kowa Yanzu": Bidiyo Ya Nuna Ayarin Motoccin Gwamnan Najeriya Ta Makale Yayin Da Ambaliyar Ruwa Ya Mamaye Titi

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164