'Yan Bindiga Ba Su Harbe Sanata Enyinnaya Abaribe Ba, Hadimin Gwamna Ya Yi Bayani

'Yan Bindiga Ba Su Harbe Sanata Enyinnaya Abaribe Ba, Hadimin Gwamna Ya Yi Bayani

  • An yaɗa wani labari a shafukan sada zumunta kan cewa 'yan ta'adda sun harbe sanatan Abia Enyinnaya Abaribe
  • An samu masu amfani da kafafen sada zumunta da suka yaɗa labarin zuwa shafukansu, sai dai babu wata jarida da ta wallafa shi
  • Sai dai hadimin wani gwamna, a ranar Alhamis 27 ga watan Yuli, ya ƙaryata labarin, wanda ya bayyana a matsayin na ƙarya mara tushe

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Umuahia, jihar Abia - Labarin da ake ta yaɗawa cewa 'yan ta'adda sun harbe sanata mai wakiltar Abia ta Kudu, Enyinnaya Abaribe ba gaskiya ba ne.

Babban mai taimakawa gwamnan jihar Legas Sanwo-Olu a kafafen sada zumunta, Ajetunmobi Ridwan Olawale ne ya musanta labarin.

Sanata Abaribe bai mutu ba
Abaribe na nan da ransa cikin ƙoshin lafiya, hadimin gwamna ya ƙaryata labarin mutuwarsa. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Sanatan ya musanta labarin da kansa

Olawale ya ce sanata Abaribe ne ya ƙaryata labarin da kansa, inda ya bayyana cewa yana nan cikin ƙoshin lafiya.

Kara karanta wannan

Kace-Nace Yayin Da 'Yan Najeriya Suka Soki Yadda Tinubu Ya Zabi Ministoci, Sun Bayyana Abin Da Ya Kamata

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani rahoti na This Day ya nuna cewa Sanata Abaribe na cikin sanatocin da ke ba da gagarumar gudummawa a batutuwa da dama da ake tattaunawa a Majalisar Dattawa.

Wata kafar labarai, Igbo Times Magazine ce ta wallafa labarin cewa 'yan ta'adda sun harbe sanatan a jiharsa ta Abia, bayan musayar wuta tsakaninsu da jami'an da ke ba shi kariya.

Sai dai Olawale a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce labarin ba gaskiya ba ne, domin kuwa Abaribe ya tabbatar masa cewa yana cikin majalisa a wani saƙo da ya tura masa.

Abaribe ya doke gwamna Ikpeazu wajen neman kujerar sanatan Abia ta Kudu

A wani labari mai alaƙa da wannan da Legit.ng ta wallafa a baya, kun karanta cewa tsohon gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sha kashi a hannun Sanata Abaribe na jam'iyyar APGA, a wajen neman kujerar sanata mai wakiltar Abia ta Kudu.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji Ta Bayyana Ainihin Dalilin Kama Sojan Da Ya Bar Musulunci Ya Koma Kiristanci

Abaribe ya samu ƙuri'u 49,693, sai Chinedu Onyeizu na jam'iyyar Labour da ya samu ƙuri'u 43,903, yayinda shi kuma Ikpeazu na PDP ya samu ƙuri'u 28,422.

Tsofaffin gwamnoni 6 da suka shiga cikin ministocin Tinubu

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan tsofaffin gwamnonin Najeriya shida da suka shiga cikin jerin sunayen mutanen da Tinubu zai naɗa ministoci.

An bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da tsohon gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike na cikin waɗanda za a naɗa ministoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel