Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Bayyana Lokacin Da Za a Bayyana Sunayen Ministocin Tinubu

Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Bayyana Lokacin Da Za a Bayyana Sunayen Ministocin Tinubu

  • Shugaba Bola Tinubu ya bayyana lokacin da sunayen ministocinsa da aka daɗe ana jira za su isa majalisa domin tantancewa
  • Opeyemi Bamidele, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, ya bayyana cewa shugaban ƙasar ya gaya masa cewa sunayen za su isa majalisa ranar Alhamis
  • Bamidele ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya gaya masa hakan ne lokacin da ya kira shi ranar Talata domin ya taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa

FCT, Abuja - Sunayen ministocin Shugaba Bola Tinubu za su isa majalisar dattawa a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli.

Opeyemi Bamidele, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa shi ne ya bayyana hakan a wajen wata lacca da ƙaddamar da wani littafi, domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa a birnin tarayya Abuja ranar Talata, 25 ga watan Yuli, jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Majalisar Dattawa Ta Dage Sanar Da Jerin Sunayen Ministocin Tinubu

Ministocin Tinubu za su isa majalisa ranar Alhamis
Ranar Alhamis sunayen ministocin Tinubu za su isa majalisa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Sanata Bamidele ya bayyana cewa Shugaba Tinubu da kansa ya gaya masa cewa sunayen ministocin za su isa majalisa ranar Alhamis, lokacin da ya kira shi a waya domin yi masa murnar cikarsa shekara 60 a duniya.

Shugaba Tinubu ya kira Bamidele a waya

Bamidele ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya kira shi da misalin ƙarfe 10:00 na safe ranar Talata, cewa ba zai samu halartar lacca da ƙaddamar da littafin ba, saboda yana son ya kammala haɗa bayanan da zai turawa majalisar nan da sa'o'i 48.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban masu rinjayen ya ambato Shugaban ƙasar yana cewa:

"Bari na gaya maka, sannan dole ka ƙarfafa min gwiwa, ina son ba zan halarci komai ba a cikin sa'o'i 48 masu zuwa saboda dole saƙo ya isa zuwa ga majalisar dattawa, saƙo mai matuƙar muhimmanci."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sanatoci Sun Taso Oshiomole Gaba Kan Zargin Sata Da Ya Yi Musu

"Shugaban ƙasa ya yi min addu'a. Mu gaya ƴan Najeriya su yi masa addu'a ya yanke hukunci mai kyau a cikin sa'o'i 24 masu zuwa ta yadda idan ƴan Najeriya suka ji sunayen ministocinsa za su ce lallai hakan ya yi."
"Sannan ku taya ni yi wa Shugaban ƙasa addu'a. Yana buƙatar kaucewa kowane irin abu da zai yi rinjaye a kansa ya yi zaɓen tumun dare."

Sanatoci Sun Taso Oshiomole a Gaba

A wani labarin kuma, an samu ƴar hatsaniya a majalisar dattawa bayan Sanatoci sun taso Sanata Adams Oshiomole a gaba busa zargin sata da ya ɗora musu.

Sanatocin sun nemi Oshiomole da ya nemi afuwa na kalaman da ya yi ko kuma su sanya shi ya fuskanci kwamitin ɗa'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel