“Allah Kadai Ne Zai Kare Shi”: Sani Ya Magantu Kan Shari’ar Da Atiku, Obi Ke Yi Da Tinubu

“Allah Kadai Ne Zai Kare Shi”: Sani Ya Magantu Kan Shari’ar Da Atiku, Obi Ke Yi Da Tinubu

  • Tsohon dan majalisa, Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa jam'iyyun adawa za su karbi hukuncin karshe da kotun zaben shugaban kasa za ta yanke
  • Alhaji Atiku Abubakar (PDP) da Peter Obi (Labour Party) suna kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023
  • Su duka yan siyasan biyu da jam'iyyunsu sun nemi a ayyana zaben a matsayin mara inganci ko kuma a bayyana su a matsayin wadanda suka lashe zaben

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Tsohon sanata wanda ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli, ya ce duk yadda hukuncin karshe ya zo a kotun zaben shugaban kasa, jam'iyyar adawa za ta karbe shi.

Da yake rubutu a shafinsa na Twitter, Sani ya ce idan kotu ta tsige shugaban kasa Bola Tinubu daga kan kujerarsa, wani babban dan siyasa a jihar Kaduna zai yi gagarumin caccaka ga tsohon gwamnan na jihar Lagas.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar Labour Ta Yi Azarɓaɓin Faɗin Abin Da Zai Faru a Ƙarshen Shari'ar Obi Da Tinubu

Sanata Shehu Sani
“Allah Kadai Ne Zai Kare Shi”: Sani Ya Magantu Kan Shari’ar Da Atiku, Obi Ke Yi Da Tinubu Hoto: Shehu Sani, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

"Allah ne kadai zai kubutar da Tinubu daga bakin tsohon gwamnan kama-karya na Kaduna": Sani

Jiga-jigan jam'iyyun adawa, Atiku Abubakar da Peter Obi sun shigar da kara inda suka nemi kotu ta soke nasarar Tinubu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ranar 1 ga watan Maris ne hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Tinubu dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben.

Ya rubuta:
"Idan Tinubu ya yi nasara a kotu sannan ta tabbatar da nasararsa, jam'iyyun adawa na iya taya shi murna ko su yi watsi da hukuncin sannan su ci gaba da harkokinsu.
"Idan hukuncin kotu ya zo da akasi a kan Tinubu sannan ya rasa kujerar shugaban kasa, Allah ne kadai zai cece shi daga bakin tsohon shugaban kama-karya na Kaduna da littafinsa na gaba "Yadda muka raya shi sannan ya ci amanar mu."

Kara karanta wannan

Aisha Yesufu Ta Nemi a Hukunta Tinubu Kamar Yadda Aka Yi Wa Mmesoma

Zanga-zangar zaman gida ba laifi bane, tilastawa mutane da ake yi wa a kudu maso yamma ne kuskure

A wani labarin kuma, tsohon sanata daga Kaduna kuma dan fafutuka, ya yi martani ga rikicin da ke addabar yankin kudu maso gabas, musamman dokar zaman gida da kungiyar fafutukar kafa kasa Biyafara ta kakabawa mutane.

Sani, sanata a majalisar dattawa ta 8, ya tuna lokacin da shi da sauran yan fafutuka suka fito da dabarar zanga-zangar zaman gida a lokacin mulkin soja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel