“Zanga-Zangar Zaman Gida Halal Ce Kuma Hanya Ce Ta Yin Zanga-Zanga Cikin Lumana”: Shehu Sani

“Zanga-Zangar Zaman Gida Halal Ce Kuma Hanya Ce Ta Yin Zanga-Zanga Cikin Lumana”: Shehu Sani

  • Shehu Sani, tsohon sanata daga jihar Kaduna ya yi bayani kan tushen zanga-zangar zaman gida a Najeriya
  • Sani ya bayyana cewa a lokacin da suke gwagwarmaya da mulkin soja, an bullo da wannan dabarar, kuma mutane sun bi ba tare da an tilasta musu ba
  • Sai dai kuma, tsohon dan majalisar ya nanata cewa ya fi gaban irin zanga-zangar zaman gida da ke gudana a yankin kudu maso gabashin Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kaduna - Shehu Sani, tsohon sanata daga Kaduna kuma dan fafutuka, ya yi martani ga rikicin da ke addabar yankin kudu maso gabas, musamman dokar zaman gida da kungiyar fafutukar kafa kasa Biyafara ta kakabawa mutane.

Sani, sanata a majalisar dattawa ta 8, ya tuna lokacin da shi da sauran yan fafutuka suka fito da dabarar zanga-zangar zaman gida a lokacin mulkin soja.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Motar da ta dauko masu zuwa 'party' ta yi karo da motar yashi, mutum 20 sun mutu

Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda suka fara zanga-zangar zaman gida
“Zanga-Zangar Zaman Gida Halal Ce Kuma Hanya Ce Ta Yin Zanga-Zanga Cikin Lumana”: Shehu Sani Hoto: Shehu Sani
Asali: Twitter

Sanatan arewan ya yi watsi da tilastawa jama'a zaman gida da kungiyar IPOB ke yi a kudu maso gabas, yana mai cewa hakan na nuna wannan ya fi gaban fafutukar mutanen da abun ya shafa.

Yadda muka fara zanga-zangar zaman gida, tsohon sanatan Arewa ya bayyana

A wani rubutu da yi a shafin Twitter a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli, Sani ya ce a lokacin fafutukarsa karkashin mulkin soja a karkashin inuwar "Campaign for Democracy", mutane sun bi manufar zaman gidan ba tare da an tilasta masu ba, hatta lokacin da yawancinsu (masu fafutuka) ke a gidan yari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sani ya rubuta:

"Zanga-zangar zaman gida halal ne kuma hanya ce ta yin zanga-zanga cikin lumana. Mun yi amfani da wannan dabarar a zamanin fafutukarmu kan mulkin soja karkashin kungiyarmu mai suna Campaign for Democracy. Jama'a sun bi don nuna goyon baya. Hatta lokacin da aka kama wasunsu aka tura su kurkuku, an bi.

Kara karanta wannan

Dakyar: Bayan shan titsiyen kwanaki a hannun DSS, tsohon gwamnan Arewa ya shaki iskar 'yanci

"Idan har sai an yi amfani da dole ko tashin hankali don mutane su bi, kamar yadfda ake yi yanzu a kudu maso gabas, toh akwai matsala a lamarinku ko fafutukarku."

Ga wallafarsa a kasa:

Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa a Abuja, cikakken bayani

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shirya wani taron gaggawa don tattauna halin da kasar ke ciki.

An shirya yin taron ne a ranar 11 ga watan Yuli, a Abuja kuma shine na farko da kungiyar za ta yi bayan babban zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng