Jam'iyyar APC Ta Tunatar Da Abba Gida-Gida Wadanda Suka Fara Siyar Da Kadarorin Gwamnati a Kano

Jam'iyyar APC Ta Tunatar Da Abba Gida-Gida Wadanda Suka Fara Siyar Da Kadarorin Gwamnati a Kano

  • Jam'iyyar APC a jihar Kano ta fito ta kare tsohon gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje daga zargin siyar da kadarorin gwamnati
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa siyar da kadarori ba baƙon abu bane a jihar domin gwamnatocin baya ma sun yi hakan
  • APC ta yi Allah wadai da rusau ɗin da Abba Gida-Gida ya ke yi a jihar inda tace hakan ba alheri bane ga jihar Kano

Jihar Kano - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano, ta yi martani kan zargin siyar da kadarorin gwamnati da ake yi wa gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa mataimakin shugaban jam'iyyar na jihar, Alhaji Shehu Maigari, a yayin ganawa da ƴan jarida ya ce ba kansu farau ba siyar da kadarorin gwamnati.

Kara karanta wannan

Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Ya Kara Jiƙa Wa PDP Aiki Kwanaki Kaɗan Bayan Rantsar da Tinubu

APC ta yi martani kan zargin siyar da kadarori a Kano
Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Guardian.com
Asali: UGC

Maigari ya bayyana cewa gwamnatocin marigayi Abubakar Rimi, marigayi Banki Zuwo, Malam Ibrahim Shekarau, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, duk sun siyar da kadarorin gwamnati a lokacin mulkinsu.

Maigari ya yi nuni da cewa gwamnan jihar mai ci na yanzu, yana da masaniya kan yadda gwamnatin Kwankwaso ta riƙa siyar da kadarori, domin ya yi masa kwamishinan ayyuka a lokacin mulkinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar ta APC ta yi kira ga waɗanda lamarin ya shafa da su nemi haƙƙin asarar da aka janyo musu a kotu, cewar rahoton Punch.

Jam'iyyar APC ta yi Allah wadai da rusau ɗin Abba Gida-Gida ya ke yi a Kano

Jam'iyyar ta kuma yi Allah wadai da wannan rusau ɗin da gwamnatin NNPP ke yi jihar, inda ta bayyana cewa hakan yana da illa ga birnin na Kano wanda ya kasance babbar cibiyar kasuwanci.

Kara karanta wannan

Wasu Manyan Jiga-Jigan PDP da Ɗumbin Mambobi Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Arewa

Jam'iyyar ta bayyana rusau ɗin da gwamnatin jihar ke yi a matsayin wata babbar annoba wacce ta janyo asarar biliyoyin nairori.

Harkokin kasuwanci musamman a manyan kasuwanni irin su, Kantin Kwari da Kofar Wambai sun tsaya cak inda aka caccaki matakin gwamnatin saboda yadda ya haddasa hargitsi, sace-sace da ƙwacen kayayyaki da sunan ganima da wasu matasa ke yi.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin birnin Kano kan wannan rusau ɗin da gwamnatin Abba Gida-Gida ta ke yi a jihar. Ibrahim Zulkiful ya bayyana cewa akwai kuskure yadda ake gudanar rusau ɗin

Ibrahim wanda ake yi wa inkiya da Meru ya ce akwai kuskure bisa rashin yadda ba a ba masu wajajen lokacin da za su kwashe su ba kawai aka kama rushe musu wajen sana'a wanda akwai dukiyoyi a ciki.

Sai dai ya nuna goyon bayansa kan a rushe dukkanin wasu wurare da aka siyar waɗanda na makarantu ne.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Matawalle Bai Bar Ko Sisi Ba a Asusun Jihar Zamfara? Gaskiya Ta Bayyana

Kamfani Ya Maka Gwamnatin Abba a Kotu, Yana Neman N10bn Saboda Ruguza Otel

Rahoto ya zo kan yadda wani kamfani ya maka gwamnatin jihar Kano a kotu kan rugurguza masa otel da ta yi.

Kamfanin Lamash Property Ltd ya garzaya kotu neman a biya shi N10bn saboda gagarumar asarar da aka janyo ya tafka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel