Daga Karshe Jam'iyyar APC Ta Bayyana Gaskiyar Abinda Matawalle Ya Bari a Asusun Gwamnatin Jihar Zamfara

Daga Karshe Jam'iyyar APC Ta Bayyana Gaskiyar Abinda Matawalle Ya Bari a Asusun Gwamnatin Jihar Zamfara

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara ta musanta cewa tsohon gwamnan jihar bai bar ko sisi ba a asusun jihar
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa gwamnatin tsohon gwamna Muhammad Bello Matawalle ta bar N20bn da $1.9m a asusun jihar
  • APC ta kuma zargi sabon gwamnan jihar na jam'iyyar PDP da nuna halin ko in kula kan matsalar tsaron da ta addabi jihar

Jihar Zamfara - Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta bayyana gaskiyar abinda gwamnatin tshohin gwamna Muhammad Bello Matawalle, ta bari a asusun jihar.

Jam'iyyar ta yi iƙirarin cewa gwamnatin Matawalle, ta bar kimannin N20.5bn da $1.9m a asusun gwamnatin jihar, rahoton Aminiya ya tabbatar.

APC ta musanta cewa Matawalle bai bar ko sisi ba a asusun Zamfara
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Kakakin jam'iyyar APC na jihar Yusuf Idris Gusau, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya zargi sabuwar gwamnatin PDP ta Dauda Lawal Dare da musanta amsar kuɗaɗen.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Zabo Malamin Makarantar Firamare a Matsayin Dan Takarar Mataimakin Gwamna a Jihar Arewa

Jam'iyyar ta kuma haɗa da yin martani kan zargin da sabuwar gwamnatin ta yi na cewa Matawalle ya yi awon gaba da wasu motocin alfarma da gwamnatinsa ta siyo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da farko dai gwamnatin Dauda Lawal ta bai wa tsohon gwamna Matawalle wa’adin kwana biyar domin ya dawo da motocin alfarma da gwamnatinsa ta siyo waɗanda aka aka cire kuɗinsu daga asusun jihar, kuma suka ɓace ɓat.

A cikin sanarwar APC ta bayyana cewa idan gwamnatin Dauda na son sanin inda motocin suke, to ma'aikatu da hukumomin gwamnati za su nema ba su nemi takurawa Matawalle ba.

APC ta caccaki sabon gwamnan

Sanarwar da jam'iyyar ta fitar ta kuma kira gwamnan a matsayin wanda bai san inda zai dosa ba.

jam'iyyar APC ta kuma zargin sabon gwamnan da shillawa zuwa Abuja da Bauchi halartar tarurruka, inda ya nuna halin ko in kula kan kashe-kashen da satar mutanen da jihar ke fama da shi.

Kara karanta wannan

PDP vs APC: Sabon Gwamna Ya Ba Magabacinsa Wa’adin Dawo Da Manyan Motocin Da Ya Sace

Gwamnan PDP Lawal Ya Ba Tsohon Gwamnan APC Wa’adin Kwanaki 5

Rahoto ya zo kan yadda gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ba magabacinsa wa'adin kwanaki biyar domin ya dawo da motocin da ya yi sama da faɗi da su.

Gwamnan ya zargi tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle, da sace motocin biliyoyin naira da gwamnatinsa ta siyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng