Ganduje Zai Mika Mulki a Ranar Lahadi, Zai Halarci Bikin Rantsar Da Tinubu

Ganduje Zai Mika Mulki a Ranar Lahadi, Zai Halarci Bikin Rantsar Da Tinubu

  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai mika mulkin jihar Kano ga zababben gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf
  • Ganduje zai mika ikon jihar ga Abba Gida-Gida a yau Lahadi, 28 ga watan Mayu da misalin karfe 9:00 na dare
  • Hakan ya kasance ne saboda gwamnan mai barin gado zai halarci bikin rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu

Gwamnan jihar Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje zai mika ragamar kula da harkokin jihar ga zababben gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf a ranar Lahadi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan labarai da harkokin cikin gida, Muhammad Garba, ya fitar a ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu a garin Kano, Premium Times ta rahoto.

Ganduje da Abba gida-gida
Ganduje Zai Mika Mulki a Ranar Lahadi, Zai Halarci Bikin Rantsar Da Tinubu Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Mista Garba ya bayyana cewa ana sa ran taron zai gudana da misalin karfe 9:00 na daren ranar 28 ga watan Mayu a gidan gwamnatin Kano.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Jerin Manyan Matsaloli 5 da Ke Jiran Tinubu da Zarar Ya Karbi Buhari

A cewarsa, kwamitin mika mulki na gwamnatin jihar ta sanar da ci gaban ga kwamitin mika mulki na zababben gwamnan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma bayyana cewa kwamitocin biyu sun gana cikin makon yayin da aka gabatarwa kwamitin zababben gwamnan da takardun mika mulki sannan an yi aiki kan ajandar bikin mika mulkin.

Ganduje zai halarci bikin rantsar da zababben shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Litinin

Kwamishinan ya yi bayanin cewa jim kadan bayan taron Ganduje zai tafi Abuja a matsayin shugaban tawagar Kano zuwa bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar Litinin.

Ya kara da cewar tafiyar gwamnan ya zama dole ne don yin daidai da wa'adin rufe filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja domin bikin rantsar da shugaban kasar.

Daga karshe ya yi kira ga jama'a da su ci gaba da yi wa addu'an samun zaman lafiya da ci gaba, rahoton PM News.

Kara karanta wannan

May 29: Manyan Batutuwa 4 Da Suka Kawo Cikas Ga Gwamnatin Buhari

Abba Gida-Gida ya gayyaci Sanusi II bikin rantsar da shi a matsayin gwamna

A wani labarin, mun ji cewa gwamnan jihar Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf ya gayyaci tsigaggen sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, zuwa wajen bikin rantsar da shi.

A cikin wasikar gayyatar wanda Abba ya sanyawa hannu mai kwanan wata 26 ga watan Mayu, zababben gwamnan ya ce zuwan Sanusi zai kara kawatar da taron kuma zai zama gagarumin gudunmawa a garesu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel