Ban San Komai Ba Kan Bangaren Ilimi Lokacin Da Buhari Ya Naɗa Ni Minista, Adamu Adamu

Ban San Komai Ba Kan Bangaren Ilimi Lokacin Da Buhari Ya Naɗa Ni Minista, Adamu Adamu

  • Ministan ilimi Malam Adamu Adamu ya bayyana cewa bai san komai ba a ɓangaren ma'aikatar ilimi a lokacin da shugaba Buhari ya naɗa shi ministan ilimi
  • Ya bayyana hakan ne yau Alhamis a Abuja a wajen taron bankwana da shugabannin ɓangarori daban-daban na ma'aikatar ilimin
  • Adamu ya bayyana cewa sai da ya yi amfani da hikinkimu ta hanyar nemo waɗanda suke da ido a ɓangaren domin samun damar yin abinda ya kamata

Abuja - Ministan Ilimi Mallam Adamu Adamu, ya bayyana cewa bai san komai ba a ɓangaren harkokin ilimi a lokacin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi ministan ilimi a shekarar 2015.

Adamu, wanda shi ne minista mafi daɗewa a kan kujera, ya bayyana hakan ne a wajen taron bankwana da ya yi da shugabannin hukumomin ma’aikatar a ranar Alhamis, Daily Trust ta yi rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ɗebo da Zafi, Ya Fallasa Masu Satar Dukiyar Talakawa a Kusa da Buhari

Adamu Adamu ya ce bai san komai ba kan bangaren ilimi a lokacin da Buhari ya ba shi minista
Adamu Adamu ya ce bai san komai ba kan bangaren ilimi a lokacin da Buhari ya ba shi minista. Hoto: 21st Century Chronicle
Asali: UGC

Ban san komai ba a ɓangaren

Ya ce an tilasta masa yin amfani da hikima ta hanyar naɗa wasu farfesoshi na ilimi da sauran nagartattun mutane, tare da kuma taimakon jami’an ma’aikatar ilimi ta ƙasa, don samun damar fara aiki da kuma kawo ci-gaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Adamu yace:

“Ban san komai ba game da fannin ilimi lokacin da aka naɗa ni minista sai dai sama-sama. Amma da Buhari ya yanke shawarar naɗa ni ministan Ilimi, sai na nemo wasu mutane don su taimaka min wajen yin aiki bisa ƙa'idojin ɓangaren ilimi saboda ni baƙo ne a fannin. Mun haɗa basirarmu tare, inda suka taimake ni sosai, kuma ina ci gaba da godiya a gare su tsawon waɗannan shekaru."

Ministan ya kuma yabawa shugaban ƙasa da ya ga ya cancanta kuma ya ba shi wannan muƙami, duk da cewa a zahiri bai shirya yin irin aikin ba.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Kunyata 'Yan Najeriya Ba," Tinubu Ya Faɗi Kalamai Masu Jan Hankali Bayan Buhari Ya Masa Abu 1

Adamu ya kara da cewa:

“Na shagaltu da bayar da shawarwari ga shugaban ƙasa kan waɗanda zai naɗa a cikin majalisarsa a shekarar 2015. Kwatsam sai ya bayyana sunana kuma iyakar abinda aka yi kenan. Mun yi aiki tare har 2019.”

Na bai wa Buhari shawara

Adamu Adamu ya kuma ce sai da ya bai wa Buhari shawara a shekarar 2019 kan ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul ta hanyar sauya wasu da waɗanda ake ganin za su fi su yin abinda ya kamata.

A cewarsa:

“A shekarar 2019, na sami shugaban ƙasa, na ba shi shawarar ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul, saboda a al'adar mafi yawan mutane, ba kasafai ba ne ake samun shugaban ƙasa ya yi aiki da ministoci na tsawon shekaru huɗu. Buhari ya yi ƙoƙarin barin ministocinsa su yi aiki tare na tsawon shekaru huɗu, saɓanin yadda ake yi wa ministoci garambawul duk bayan shekara biyu.”

Kara karanta wannan

Abun Hawaye: Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Ministoci Kalamai Masu Ratsa Zuciya A Taron Bankwana

Sai dai Adamu ya ce duk da waccan shawarar da ya bai wa Buhari ta yi wa ministoci garambawul, ya san da wuya ne ya yi hakan, in ji jaridar The Sun.

Adamu ya kuma ce duk da hakan sai da ya kawo masa sunayen waɗansu da yake ganin za su iya taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci-gaba a cikin gwamnatinsa.

Gwamnoni takwas da ka iya samun muƙamin minista a gwamnatin Tinubu

A wani labarinmu na baya, mun kawo muku sunayen wasu gwamnonin APC takwas da ake ganin Tinubu zai bai wa muƙaman ministoci a gwamnatinsa.

Dukansu dai gwamnoni ne da ke kammala wa'adinsu a ranar 29 ga watan Mayu ɗin nan mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel