Ina Fatan Daura Ba Zata Muku Nisa Ba Bayan Mun Sauka Mulki, Buhari Ga Ministoci

Ina Fatan Daura Ba Zata Muku Nisa Ba Bayan Mun Sauka Mulki, Buhari Ga Ministoci

  • Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi bankwana da Minsitoci a taron FEC na karshe da ya jagoranta yau Laraba
  • Buhari ya faɗa musu kalamai masu ratsa zuciya, inda ya ce ya shirya karban duk wanda Daura ba ta masa nisa ba
  • A jawabin Buhari, ya ce bayan sauka daga mulki zai samu isasshen lokacin aiwatar da abubuwa da dama

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce a shirye yake ya karɓi bakuncin Ministocin ba basu hangi mahaifarsa, Daura, jihar Katsina da nisa ba bayan mulki ya ƙare ranar 29 ga watan Mayu.

Daily Trust ta ce shugaban ya bayyana haka ne a wurin taron majalisar zartarwa (FEC) na bankwana da ya gudana a fadar Aso Villa ranar Laraba.

Taron FEC na karshe.
Ina Fatan Daura Ba Zata Muku Nisa Ba Bayan Mun Sauka Mulki, Buhari Ga Ministoci Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Buhari ya ce bayan sauka daga mulki wanda ya shafe tsawon shekaru 8, zai samu isasshen lokacin da zai kula da Shanunsa da yake kiwo a Daura.

Kara karanta wannan

"Zan Koma Gona Ko Aikin Ɗan Jarida Bayan Na Sauka Mulki," Gwamnan Arewa Ya Yi Magana Mai Ban Tausayi

Shugaban ƙasa mai barin gado ya ce zai samu nutsuwa da farin ciki idan ya samu lokacin gudanar da wasu harkokin da hakan ba ta samu ba tun lokacin da ya shiga Ofis a watan Mayu, 2015.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ruwayar Vanguard, Buhari ya ce:

"Ina ƙara gode wa Allah wanda ya bamu kwarin guiwa kuma ya haɗa mu wuri ɗaya zan tsumayi kowane daga cikinku, idam Daura ba ta muku nisa ba domin ba zan dawwama a matsayin shugaban ƙasa ba."
"Zan yi farin ciki idan na samu lokacin aiwatar da abubuwa da dama da ban samu damar yi ba tun ranar 29 ga watan Mayu, 2015. Ɗaya daga ciki shi ne kiwata garken shanu na."
"Baki ɗayammu, ina mana fatan Alkairi da kuma fatan jin labari mai daɗi a duk lokacin da aka ambaci sunayenmu. Muna ƙara godiya ga Allah tare da Addu'ar Allah ya albarkaci kasar mu Najeriya."

Kara karanta wannan

"Na Yafe Maka": Gwamnan Arewa Ya Aike Da Sako Mai Girma Ga Shugaba Buhari

Daga karshe, Muhammadu Buhari ya yaba da ƙwazon Ministocin da kuma ƙoƙarin aiki tare da juna duk da kalubalen da suka fuskanta.

Ya kuma roke su da su goyi bayan gwamnatin zababɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda zai karbi ragamar mulki nan da 'yan kwanaki.

Ku Ci Gaba da Zama Kan Mukamanku Har Zuwa Ranar Karshe, Buhari Ga Ministoci

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya umarci ministoci su koma Ofis har zuwa ranar da zai miƙa mulki ga sabuwar gwamnati.

Yayin taron bankwana da ya gudana yau a fadar shugaban ƙasa, Buhari ya buƙaci Ministocin su ci gaba da ayyukan ofishinsu zuwa ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel