29 Ga Watan Mayu: Ganduje Ya Gabatar Da Rahoton Mika Mulki Ga Abba Gida-Gida

29 Ga Watan Mayu: Ganduje Ya Gabatar Da Rahoton Mika Mulki Ga Abba Gida-Gida

  • Gwamna Abdullahi Ganduje ya mika rahoton mika mulki ga zababben gwamna mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf
  • Gwamnati mai barin gado ta jihar Kano ta jaddada kudirinta na tabbatar da ganin an mika mulki ga Abba Gida-Gida cikin kwanciyar hankali
  • Kwamitin jam'iyyar NNPP ya ce zai duba rahoton sannan ya yi yan gyare-gyare a duk inda bukatar hakan ya taso

Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta gabatar da rahoton mika mulki ga zababben gwamna, Injiniya Abba Kabir Yusuf, Daily Trust ta rahoto.

A wani dan takaitaccen taro da ya gudana a gidan gwamnatin Kano, Ganduje wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya jaddada jajircewarsa na tabbatar da mika mulki cikin lumana, rahoton Solace base.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Jiga-Jigan Jam'iyyun Adawa Da Tinubu Zai Naɗa Bayan Rantsarwa

Taron kwamitin mika mulki na jihar Kano
29 Ga Watan Mayu: Ganduje Ya Gabatar Da Rahoton Mika Mulki Ga Abba Gida-Gida Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ganduje ya bukaci Abba Gida-Gida ya yi nazari kan rahoton

Gwamnan ya bukaci gwamnati mai zuwa da ta yi nazari kan rahoton mika mulkin sannan ta yi jawabi a inda ya kamata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har ila yau, gwamnan ya jinjina ma mambobin gwamnati mai barin gado kan samar da rahoton wanda ya kunshi duk bangarori na jihar.

A jawabinsa, zababben gwamnan jihar wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin mika mulki na NNPP, Dr Abdullahi Baffa Bichi, ya bayyana cewa kwamitinsa zai gabatar da rahoton ga gwamna mai jiran gado sannan ya dawo da duk wani nazari da suka yi idan har akwai.

"A wannan lokaci, muna da awanni 105 ne kacal na mika mulki a jihar Kano a hukumace, saboda haka mun himmatu don ganin an mika mulki cikin lumana saboda ra'ayin Kano da mutanenta."

Kara karanta wannan

Zababben ‘Dan Majalisa Zai Kinkimo Aiki, Yana So a Binciki Buhari Bayan Ya Sauka

Wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, babban sakataren labaran zababben gwamnan jihar Kano ya fitar, ya bayyana cewa za a sanar da jama'a cikakken bayani game da bikin rantsarwar bayan an cimma yarjejeniya tsakanin gwamnati mai barin gado da mai shigowa.

2023: Ortom ya magantu kan yan takarar da G5 suka marawa baya a zaben shugaban kasa

A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya ce Peter Obi na jam'iyyar Labour Party shine dan takarar shugaban kasa da ya marawa baya a zaben 2023.

Ortom ya kuma bayyana cewa sauran takwarorinsa na gwamnonin G5 sun marawa Bola Tinubu baya ne kamar yadda suka cimma matsaya na raba kafa tsakanin yan takarar biyu wadanda suka fito daga yankin kudancin kasar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel