EFCC Ta Ƙaddamar Da Bincike Kan Gwamnoni 28 Da Mataimakansu Gabanin 29 Ga Watan Mayu

EFCC Ta Ƙaddamar Da Bincike Kan Gwamnoni 28 Da Mataimakansu Gabanin 29 Ga Watan Mayu

  • Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), ta kaddamar da wani gagarumin bincike a kan gwamnoni 28 cikin 36 na Najeriya gabanin 29 ga watan Mayu da za a miƙa mulki
  • 18 daga cikin gwamnonin da za a gudanar da bincike a kansu za su kammala wa’adinsu na biyu ne a ranar 29 ga watan Mayu
  • Ɗaya daga cikin gwamnonin zai kammala wa’adinsa na farko, a yayin da 10 daga ciki kuma aka sake zaɓar su, za su ci gaba da wa’adinsu na biyu daga ranar 29 ga Mayu

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa EFCC, ta ƙaddamar da wani gagarumin bincike kan gwamnoni 28 da mataimakansu gabanin miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Gwamnonin da ake bincike su ne waɗanda suka rasa kariyar da kundin tsarin mulki ya ba su na hana gurfanar da su a gaban ƙuliya cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, in ji rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

"Zan Koma Gona Ko Aikin Ɗan Jarida Bayan Na Sauka Mulki," Gwamnan Arewa Ya Yi Magana Mai Ban Tausayi

EFCC za ta binciki gwamnoni 28 da mataimakansu bayan 29 ga watan Mayu
EFCC za ta binciki gwamnoni 28 da mataimakansu bayan 29 ga watan Mayu. Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Adadin gwamnonin da EFCC za ta bincika bayan miƙa mulki

A cewar wata sanarwa da ke ƙunshe a wata takarda, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa na bibiyar aƙalla gwamnoni 28 da mataimakansu daga cikin 36 da muke da su a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Aƙalla gwamnoni 18 ne cikin 28, tare da mataimakansu hukumar ta EFCC ke nema ruwa a jallo waɗanda ke shirye-shiryen barin ofis da zarar sun kammala wa’adinsu na biyu a ranar 29 ga watan Mayu.

An ce ɗaya daga cikin gwamnonin zai bar ofis ne bayan kammala wa’adinsa na farko, 10 daga cikinsu sun sake lashe zaɓensu, kuma ana sa ran za su yi mulki na tsawon shekaru 4 masu zuwa.

EFCC ta aikawa da CCB wasika

An samu labarin cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta rubutawa hukumar kula da ɗa'ar ma'aikata (CCB) takardar neman takardun bayyana kadarorin gwamnonin, kamar yadda aka samu daga tattaunawar da hukumomin biyu suka yi.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tura Wani Dattijo Gidan Yari Saboda Sarrafa Kwandala Da Ficika Zuwa Kayan Ado A Kano

Sai dai babu wani cikakken bayani kan abinda EFCC ke tuhumar gwamnonin a kai, amma hukumar ta bayyana a cikin wasiƙar da ta aika wa shugaban CCB, Mohammed Isah, cewa ana buƙatar takardun bayyana kadarorin ne domin samun sauƙin gudanar da binciken kan gwamnonin.

Wasiƙar ta EFCC na ɗauke da kwanan wata 11 ga watan Afrilu, mai ɗauke da sa hannun wani jami’in hukumar a madadin shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa.

Gwamnoni biyar da suke da matsala da zaɓaɓɓun gwamnonin Jihohinsu

A baya mun kawo labarin wasu gwamnoni guda biyar da suke da matsala da zaɓaɓɓun gwamnonin jihohinsu, wanda hakan ke sa ake ganin ba za su yi abinda ya kamata wajen miƙa mulki ba.

Saɓanin da yawancinsu suke samu na da alaƙa da binciken da zaɓaɓɓun gwamnonin ke shirin yi kan yadda aka ɓatar da kuɗaɗen jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel