Zababben Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani Ya Yi Nadinsa Na Farko

Zababben Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani Ya Yi Nadinsa Na Farko

  • Sanata Uba Sani, zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kaduna ya sanar da yin naɗin muƙamin sakataren watsa labarai
  • Sanatan ya bayyana Muhammad Lawal, mai taimakawa gwamna El- Rufai kan harkokin siyasa, a matsayin wanda zai riƙe ƙujerar
  • Lawal yana da ƙwarewa sosai a ɓangarori da dama, wanda a cewar Uba Sani hakan ya sanya ya cancanta ya riƙe muƙamin

Kaduna - Sanata Uba Sani, zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kaduna, ya sanar da naɗinsa na farko, kwanaki kaɗan kafin a rantsar da shi, inda ya bayyana Muhammad Lawal, a matsayin sakataren watsa labaransa.

A cewar rahoton Tribune, Uba Sani ya yi duba ne da ƙwarewar da Lawal ya ke da ita, a ɓangarori daban-daban.

Uba Sani ya nada sakataren watsa labarai
Muhammad Shehu Lawal, sakataren watsa labarai da Uba Sani ya nada Hoto: Tribune.com
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu, zaɓaɓɓen gwamnan na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya bayyana cewa naɗin Muhammad Lawal zai fara aiki ne daga ranar Talata, 23 ga watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Ɗalibin Jami'a a Najeriya Ya Faɗi Ya Mutu Ana Tsaka da Wasan Kwallo

Muhammad Lawal yana da gogewa sosai

Lawal ya yi digirinsa na farko kan siyasa a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria, sannan ya yi digirin digiri a ABU kan International Affairs and Diplomacy (MIAD), san ya yi wani digirin digir kan Conflict, Peace and Strategic Studies, a jami'ar jihar Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon sakataren yana da satifiket da dama waɗanda suka haɗa da Interfaith Conflict Resolution and Conflict Analysis daga cibiyar ƙasar Amurka ta Institute of Peace, Washington, DC.

Sannan yana da satifiket a ɓangaren Monitoring and Evaluation daga cibiyar Global Health Learning Centre, Baltimore, USA.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Muhammad Shehu Lawal ya riƙe matsayin mai taimakawa na musamman ga gwamnan jihar Kaduna kan harkokin siyasa daga shekarar 2019 zuwa 2023.
"Ya taka muhimmiyar rawa wajen shiryawa da aiwatar da tsare-tsaren watsa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na jihar Kaduna da na yankin Arewa maso Yamma na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bola Tinubu Ya Sanya Labule Da Tsohon Firaministan Burtaniya, Bayanai Sun Fito

Tambuwal Ya Yi Sabbin Nade-Nade Masu Muhimmanci

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto mai barin gado, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi wasu sabbin muhimman naɗe-naɗe yana dab da barin mulki.

Tambuwal ya naɗa wasu manyan jami'an makarantun gaba da sakandire na jihar da babban sakataren hukumar kula da lafiya ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel