Ban Damu da Rantsar da Tinubu Ba, Kotu Za Ta Iya Karban Mulki Ko da an Rantsar da Shi – Atiku

Ban Damu da Rantsar da Tinubu Ba, Kotu Za Ta Iya Karban Mulki Ko da an Rantsar da Shi – Atiku

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce bai damu da rantsar da Tinubu da za a yi ba
  • Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Talata 23 ga watan Mayu ta bakin lauyansa, Chris Uche a Abuja
  • Ya ce ko da an rantsar da Tinubu, kotu ta na da ikon rusa zabensa da ke cike da kura-kurai da magudi

Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce bai damu ba ko kadan don za a rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu kafin kammala shari'ar karar da suka shigar.

Atiku ya fadi hakan ne a ranar Talata 23 ga watan Mayu ta bakin lauyansa, Chris Uche (SAN) jim kadan bayan sauraran karar korafe-korafen zabe a kotun da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yanke Hukunci, Ta Baiwa Peter Obi Wa'adin Da Zai Gabatar da Shaidu Kan Nasarar Tinubu

Zababben shugaban kasa Tinubu, da Atiku Abubakar
Atiku ya shigar da kara kotu kan zaben Tinubu a matsayin shugaban kasa. Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Ya ce ko da an rantsar da Bola Tinubu, kotun tana da karfin ikon da za ta rushe zaben da ya kawo shi ofishin shugaban kasa, yayin da ya ba da tabbacin cewa za su karbi mulki a hannun Tinubu, Vanguard ta tattaro.

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ana tambaya ta akan ranar rantsarwa, ina son tabbatar muku cewa rantsarwa biki ne kawai da ba zai hana kotu yin komai ba.
“Rantsarwa kawai ya shafi wanda ya yi rantsuwar ne ba kotu ba.
“Kotu ta bai wa jam’iyyu lokaci su kawo korafinsu, tabbas wannan lamari zai sa a kammala karar da wuri."

Atiku ya bukaci kotu ta rushe zaben Tinubu

Atiku, a cikin karar da ya shigar, ya ce Tinubu da aka sanar a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa bai inganta ba saboda karya dokokin zabe da ya yi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kotun Koli Ta Tsaida Ranar Sauraron Shari’ar PDP v Tinubu da Shettima

Rahotanni sun bayyana Atiku na cewa zaben Tinubu akwai kura-kurai saboda zargin sa da ake yi akan cin hanci da rashawa.

Bayan rokan kotun da ta sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zabe tun da shi ne ya kasance na biyu a zaben, Atiku da jam’iyyarsa ta PDP sun bukaci kotun ta kwace takardar shaidan da hukumar zabe ta bai wa Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa.

Atiku Ya Ɗauki Manyan Lauyoyi 19 Don Kwace Nasara Daga Tinubu

A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya roki lauyoyinsa da su kwato musu mulki a kotu.

Atiku ya dauki hayar manyan lauyoyi 19 don kalubalantar zaben da aka gudanar a farkon wannan shekarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel