Kwankwaso Ya Yi Magana Kan Ganawarsa da Bola Tinubu a Faransa

Kwankwaso Ya Yi Magana Kan Ganawarsa da Bola Tinubu a Faransa

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce tabbas ya gana da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Faransa
  • Kwankwaso, jagoran NNPP mai kayan marmari, ya ce zai fitar da cikakken bayani kan tattaunawar ranar Alhamis
  • Ana ganin wannan zama na manyan yan siyasan biyu ka iya jawo Kwankwaso zuwa jam'iyyar APC mai mulki

Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023 karkashin inuwar jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, Rabiu Kwankwaso, ya tabbatar da rahoton cewa ya gana da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.

A wata hira da kafar watsa labarai TRT Afrika, tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso, ya ce ba zai bayyana abinda suka tattauna ba sai ranar Alhamis mai zuwa.

Kwankwaso da Tinubu.
Kwankwaso Ya Yi Magana Kan Ganawarsa da Bola Tinubu a Faransa Hoto: RMK, ABAT
Asali: UGC

Idan baku manta ba, shugaban Najeriya mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Kwankwaso, jagoran NNPP da kuma tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi a ƙasar Faransa ranar Talata.

Kara karanta wannan

Assha: Da izinin Ganduje fa Tinubu ya gana da Kwankwaso, dan majalisa ya tono sirri

Takaitacciyar hira da Kwankwaso

Yayin da aka tambaye shi kan menene gaskiyar ganawar da aka ce ya yi da Tinubu a Faransa, Kwankwaso ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Eh haka ne, amma ba zan yi dogon jawabi a yanzu ba sai zuwa ranar Alhamis, zamu fitar da cikakken bayani kan ganwar. Kuma mun fara ganawa kenan, ku bari mu gama zaku ji komai."

Haka nan yayin da aka tambaye shi har tsawon kwana nawa zasu kwashe suka wannan tattaunawa, tsohon gwamnan ya jaddada cewa mutane su yi hakuri zuwa lokacin da zasu gama.

Wannan ganawa dai ta haddasa cece kuce da martani kala daban-daban a faɗin Najeriya, inda aka fara raɗe-raɗi da yuwuwar Kwankwaso ya koma APC.

Haka zalika wasu majiyoyi sun nuna cewa Bola Tinubu ya yi wa tsohon gwamnan tayin kujerar Minista a gwamnatinsa, wacce zata kama aiki ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Sharri aka min: Ganduje ya yi karin haske kan faifan muryarsa da ke yawo na sukar Tinubu

Wani jigon NNPP a Kano, Sa'idu Abdullahi, ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa ba abin mamaki bane don Kwankwaso ya zauna da Tinubu idan aka yi la'akari ta tarihin siyasarsu.

Malam Sa'idu ya ce manyan 'yan siyasan biyu sun yi mulki lokaci ɗaya a Legas da Kano daga 1999 zuwa 2003, kuma tun a wancan lokaci sun ƙulla alaƙar abota a tsakaninsu.

A kalamansa, ya ce:

"Banga abun magana ba kan tattaunawar da maigida ya yi da Tinubu, mun san abokan juna ne tun lokacin da suka riƙe gwamna a Legas da Kano tsakanin 1999 zuwa 2003."
"Abu ɗaya da zan ce Kwankwaso da Tinubu suna girmama juna, kuma shi zababben shugaban ƙasa ya san wasu kyawawan manufofin Maigida, muna fatan hakan ya zama mafi Alheri ga Najeriya baki ɗaya."

Gaskiya ta fara fitowa

A wani rahoton kuma kun ji cewa Gaskiyar Bayanan Zaman Kwankwaso, Tinubu, da Sanusi a Faransa Sun Fara Bullowa

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Muhimman Bayanai Sun Fito Yayin da Bola Tinubu Ke Shirin Dawowa Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa Kwankwaso ya ɗauki dogon lokaci yana ganawa da shugaba mai jiran gado, Bola Tinubu, ba tare da kowa ya sani ba a Faransa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel