Lokacin Mu Ne: Matasan Kiristocin Arewa Sun Fada Wa Tinubu Wanda Suke So Ya Nada Mukamin SGF

Lokacin Mu Ne: Matasan Kiristocin Arewa Sun Fada Wa Tinubu Wanda Suke So Ya Nada Mukamin SGF

  • Kungiyar matasan Kiristoci ta roki Bola Ahmed Tinubu da ya bai wa Lalong matsayin SGF
  • Kungiyar ta ce gwamna Simon Lalong shi ya cancanci wannan matsayi duba da irin kwarewarsa
  • A cewar matasan bai wa Lalong wannan matsayi zai taimaka wurin sakawa yankin nasu

Jihar Plateau - Kungiyar Matasan Kiristoci a Najeriya ’Young Christian Forum’ ta bukaci zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya bai wa Arewa maso Tsakiya mukamin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF).

Kunigyar ta yi wannan rokon ne a babban taron ta da ta yi a jihar Kaduna a ranar Laraba 17 ga watan Mayu.

Lalong/Matasa
Kiristoci Sun Bukaci Tinubu Ya Bai Wa Lalong Matsayin ‘SGF’ . Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Kungiyar ta bukaci Bola Tinubu da ya zabi gwamnan jihar Plateau Simon Bako Lalong a matsayin sakataren gwamnatinsa na tarayya, cewar gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Alkawarin da Amurka Tayi wa Najeriya da Sakataren Gwamnati Ya Kira Tinubu a Waya

A cewar matasan, zaban Lalong a wannan mataki zai taimaka wurin kawo sauyi a siyasa da kuma daidaita addini a bangarorin gwamnati da dama na kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban kungiyar, Nathaniel Agada wanda ya yi jawabi ga ‘yan jaridu yace bai wa Lalong wannan matsayi zai daidaita bambance-bambancen da ake samu a kasar musamman ta fannin addini ganin cewa shugaban kasa da mataimakinsa duka Musulmai ne.

Matasan suka ce an maida su saniyar ware a Najeriya

Ya kara da cewa Kiristoci musamman ‘yan Arewa maso Tsakiya sun cancanci wannan matsayi saboda a saka musu ganin yadda aka maida su saniyar ware a harkokin gwamnati tsawon shekaru.

Mista Agada ya ce kungiyar ta zabi gwamna Simon Lalong ne bayan duba dacewarsa a matsayin sakataren gwamnatin tarayya saboda irin ci gaba da ya kawo tun lokacin da yake shugaban majalisar jihar Plateau.

Kara karanta wannan

APC: Gwamnoni 5 a Arewa Sun ki Amincewa da Yadda Aka yi Kason Kujerun Majalisa

A lokacin da ya zama gwamnan jihar Plateau ya kawo abubuwan ci gaba wa jihar wadanda ba za su misaltu ba, kafin daga bisani ya zama shugaban gwamnonin Arewacin Najeriya gaba daya.

Simon Lalong na Plateau Ya Tunkuri Ƙasa a Takarar da Yayi Ta Sanata

A wani labarin, Darakta janar na yakin neman zaben Bola Tinubu, Simon Lalong yasha kasa a kokarinsa na shiga majalisar dattawan Najeriya ta 10.

Lalong ya sha kaye ne bayan Hukumar Zabe mai zaman kanta ta bayyana sakamakon zabubbuka da aka gudanar a jihar, a ranar 25 ga watan Faburairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel